HALIN DA JAGORA KE CIKI: An Gudanar Da Muzaharar Nuna Rashin Amincewa A Garin Saminaka

HALIN DA JAGORA KE CIKI: An Gudanar Da Muzaharar Nuna Rashin Amincewa A Garin Saminaka

 🇳🇬MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS
UPDATES:
 Daga Wakilinmu
 Ibrahim Almustapha Saminaka

Sakamakon rashin lafiyar da Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) yake fama da ita cikin kwanakin nan, Yau Litinin 8 ga watan July 'yan uwa musulmi na garin Saminaka sun sake gudanar da Muzaharar kira ga azzalumar gwamnatin Buhari ta gaggawa sakin Sheikh Zakzaky domin yaje neman lafiyarsa da na matarsa.



 An fara gudanar da Muzaharar ne da misalin karfe 4:30pm daga cikin babban tasha dake garin Saminaka, inda aka hau babban titin da ya nufi Jos da Kaduna. Matasa maza da mata ke fadin cewa "A saki musu Jagoransu domin ya fita wajen neman lafiyarsa"








 An rufe Muzaharar ne a kasuwar 'yan gwari dake garin na Saminaka. Wanda Malam Umar Uba Saminaka yayi jawabai masu gamsarwa sannan ya rufe Muzaharar da addu'a. An kammala Muzaharar lafiya ba tare da wata matsala ba.

Daga Wakilinmu
 Ibrahim Almustapha Saminaka
- 8/July/2019
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post