Daga Muhammad Ibraheem Zakzaky
A wannan Asabar din 6 ga watan Yulin 2019, na samu haduwa da Mahaifina da Mahaifiyata. Kamar dai yadda a ka bayyanawa mutane, rayuwar Mahaifina na fuskantar barazana daga gubar da ta tasirantu a cikin jininsa. A sanadin wannan, dukkan kwararrun da muka tuntuba dangane da rashin lafiyan sun bayar da shawarar dole a gaggauta kwantar da Mahaifina a asibitin da ke da wadatattun kayan aiki domin a iya ceton ransa. Wannan a na maganar sama da wata guda da ya shige, amma har yanzu din nan shiru ka ke ji, ba abin da a ka yi a kai.
Mahaifiyata kuwa, wacce tun da dadewa an san irin cututtukan da ke damunta, har wa yau babu wata kulawa da ta samu kamar yadda kwararru suka yi bayani. Irin radadin da ta ke fama da shi daga cututtukan a bayan duk wata, ya dawo yana addabarta a kowacce rana. Kuma fa har yanzu ba a dauki hanyar magance ko daya cikin wadannan cututtuka ba.
Da muka hadu, bayan irin tabarbarewar rashin lafiyar mahaifina da muka iya lura da shi kamar yadda hakoransa suka sauya suka yi bakikkirin, ya sanar da ni cewa, lamarin jikinsa ya sake tabarbarewa ne fiye da lokutan baya da muka ziyarce shi. Abin ban tsoron shi ne, jikinsa ya fara yin yanayi sak da lokacin da ya kamu da matsalar shanyewar barin jiki a watan Janairun 2018. Wanda a baya, sai lokacin bayan lokaci ne yake fama da matsanancin radadi, amma yanzu kusan kullum ne.
Duk da dai bana son cire tsammani, amma a irin halin da a ke ciki, ina tunanin zai yi min wahala na iya ceton rayuwar Mahaifina, saboda duk wata hanya da muka bi wurin ganin an ceci rayuwarsa sai an dakusheta ko an haifar mata da matsala da gangan. A shekarun baya na fadi cewa, akwai shirin kashe Mahaifana ta hanyar yin biris da lamarin tabarbarewa rashin lafiyarsu, duk da a wancan lokacin ban san irin tsanantar cutar nasu ba. Kawowarsu yanzu a raye, abin al’ajabi ne wannan daga Allah.
Daga bayanan da na tattara daga wurin qwararru a makonnin da suka gabata, cike da takaici nake son na sanar da cewa, lokacin da a ke da bukata don ceto rayuwarsu kusan ya wuce. Wannan ba komi bane face kokarin yin kisan kai da gangan, wanda kuma an kusa cimma manufa. Wanda kuma makasan a shirye suke da su aikata kisan kansu ba tare da wata damuwa ba.
— Mohammed Ibraheem Zakzaky
Tare da Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates tare da -Idishia Jos.
Tags:
Jawaban Sheikh Zakzaky