GASKIYAR ABUNDA YA FARU A WAQI'QR ABUJA YAU LITININ




Waki’ar Abuja ta yau Litinin
a jaridun kasashen waje…..
Abin da ya faru a yau Litinin a birnin Abuja
ya jawo hankalin manema labarai a ciki da
wajen Nigeria, ta yadda kanun jaridu da
mujallu suka dauki labarin a shafukan su
na farko.

A yau ne dai jami’an tsaron Nigeria suka
aukawa muzahara ta lumana da aka
gabatar a birnin na Abuja wadda aka saba
gabatarwa a kullum don ci gaba da kira ga
gwamnati data gaggauta sakin Malam [H].
Sakamakon afkawa muzaharar data iso
bangaren Federal Secretariat an samu
shahidai akalla shida kuma wasu da dama
sun sami raunuka.

Cikin wadanda jami’an tsaron suka kashe
harda yaro dan kasa da shekaru goma
kamar yadda rahotanni suka nuna. Haka
nan kuma hotuna mara sa motsi dana
Bidiyo sun nuna jami’an tsaro suna
kwashe gawarwakin wadanda suka harba suna tafiya dasu

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post