Da Adalci ake gane Musulmi kirki.

Da  Adalci ake gane Musulmi kirki.

Daga Sannan marubucin nan  na social media @Almuhajir
Dr,Almuhajir


Why Shiah

Ni fa har yanzu a Najeriya ba abunda yake kulle mun kai, ya hanani fashin baki kamar lamarin gomnati da Yan Shiah, shi yasa kullum tambaya nake yi me yasa ake hallaka Yan Shiah ne?

1- Idan tawaye ne ga Yan IPOB, Nnamdi Kanu bayan ya gama tsinewa Najeriya da Yan Najeriya, ya jawo har rundunar Sojan Najeriya aka sauke masu, Amma an bada belin shi. Bayannan ya karya dokar belin ya tsere amma har ya zu an kasa kamo shi adawo da shi duk da muna da bilateral agreement na extradition da Ingila

2- In zangazanga ne a kasar nan aka yi fuel subsidy, shugaban kasa bashi da hujjar yaki da zangazanga, duba da zangazangar zaben shi da akace an murde a 2003,2007,2011. Ga bring back our girls dss,

3- Idan zagin Buhari ne ga wasu chan ma sun bi shugaban kasa da placards a Ingila suna ta zagin shi gaban idon shi. Kuma kullum sai zagin shi akeyi a TV, Radio Facebook dss. idan yaji haushin zagin me zai hana shi kaisu Kara kotu?

4- Abun mamaki shine wasu sai suce saboda suna zagin Sahabbai, to Ina ruwan constitution din Najeriya da sahabin Annabi. Wasu na tsammani "the labor of our heroes fast" din ana nufin sahabbai ne. To bari kuji a constitution din Najeriya Sardauna da Azikwe da Tafawa Balewa sunfi sahabbai daraja. Saboda haka cewa Dan Sandan Najeriya yana kare sahabbai ma wauta ce kawai.

5- Me yasa aka kasa Kai Zakzaky kotu har yanzu ne, me suke tsoro da shine? Shi Zakzaky yafi karfin Sharia ne?

Rashin amsar wadannan tambayoyi suka sa nake da tabbas cewa zalumta Yan Shiah ake yi a kasar nan.
✍️
Ishaq sagir magaji

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post