BA ZA SU IYA KASHE SAYYEED (H) BA IN BA YA GAMA AIKIN DA ALLAHYA 'DORA MASA BA!!!

BA ZA SU IYA KASHE SAYYID (H) BA IN BA YA GAMA AIKIN DA ALLAH YA 'DORA MASA BA !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Babu kokwanto, Allah ya dorawa Sayyid (H) wani aiki mai wuyan da ba kowa ne ke iya yinsa ba, kuma kaya ne da ba kowa ke iya daukarsa ba.
Al'marin tajdidin addini aiki ne na zababbun bayin Allah wadanda yake zabarsu musamman din don yin wannan aiki nasa.
Shi yasa duk wani Annabin da Allah ya aiko sai an cutar dashi kan wannan aiki akan idonsa, kuma ba wai don ba ya sonsu bane ya bari ake cutar dasu.
Babu wani dan saqo daga Allah Annabi ne ko kuma Mursali da yayi wannan aiki ya gama lafiya ya koma ga Ubangijnsa ba tare da an cutar dashi ba.
Gwargwadon matsayin mutum a wajen Ubangiji shine gwargwadon jarrabawar da za ayi masa, kuma hakan shi zai sa ya cancanci gidan da aka tanadar masa a Aljannah.
Annabi Ibrahim (A S) bai sami matsayin da ya samu ba har sai da aka jarraba shi kuma ya cinye jarrabawar 100%.
Da ace harbi shine mutuwa ba tare da sai lokaci yayi ba, to, da yanzu Sayyid (H) ya fada cikin kundin tarihi. Hakama guba tana tasiri ne idan taci karo da ajali.
Na'am, duk abu biyun nan suna sanadi, amma sai sunci karo ne da cikar ajali.
Amma hakan ba wai yana nufi a dakatar da motsi ko addu'o'in da ake yi bane, sai dai komai na tafiya ne gwargwadon yadda Allah ya hukunta.
Tare da Ado Isah Guda.
FREE SAYYID ZAKZAKY (H) !!!

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post