Ba Gudu Ba Ja Da Baya: BA ZAMU DAI NA FADA BA, BUHARI AZZALUMI NE KA SAKAR MANA JAGORANMU.

                 Sheikh Adamu Tsoho Jos

Daga shafin Ma'asumah Nigerian News Updates, Tare da -Idishia Jos.

"A cigaba da fafatawa da ganin cewa Malam ya fito daga hannun azzalumin shugaba Buhari a yau wannan Juma'a Allah ya kawo mu wannan masallaci domin isar da sakon zalunci da aka yiwa Malam da 'Ya'yansa da Almajiran sa, duk da yake na fahimci cewa wajen fitowan mu daga masallaci al'umma basu fahimci mu ba, wasu na cewa to muje "Villa" wasu ma suna ta maganganu na cewa kuskurene a matsayin ka na musulmai. To ku sani shi musulmi Manzon Allah (S) ya wajabta mana sanin halin da 'yan uwan mu musulmi suke ciki. Har yazo a ruwayan hadisi Manzon Allah (S) yana cewa "Duk wanda ya wayi gari bai damu da halinda sauran 'yan uwansa musulmi yake ciki ba, baya tare damu."

Sheikh Adamu Tsoho ya kara da cewa Don haka ya zamo lazim al'umman musulmi susan menene yake gudana dangane da 'yan uwansu musulmi a wannan kasa da ma sauran kasashen duniya, saboda Allah ya bai yanar mana cewa " mu yan uwan junane mumunai, kamar yadda suke cewa muje "Villa" to munje "Villa" kuma bazamu bar "Villa" ba har sai randa aka saki Malam a halinda yake ciki da sauran Almajiran Malam da halinda suke ciki. Ba zamu gushe ba muna cewa Free #FreeZakzaky, kuma har ila yau ba zamu gushe ba muna cewa Buhari azzalumi ne ka sakar mana jagoranmu.

"Sakon Sheikh Adamu Tsoho Ga su Musulmai" Kuma kuskure ne suke cewa ba ruwansu da sauran mutane sabida Manzon Allah (S) yana cewa duk wanda bai taimakawa dan uwansa musulmi ba a lokacin da yake neman taimako to ya tabbata wannan mai neman hakkin shi kadai ne musulmi, hakki ne akan musulmai su fito suyi magana su yi inkarin zaluncin Buhari suyi inkarin ta'addancin da sojoji sukayi akan Malam da Almajiran sa da ma sauran ta'addancin da ake yiwa musulmai a wannan kasa, ko ba komai a matsayin mu na Almajiran Malam in ma baka san zaluncin da aka yiwa malam ba to, yau fitowanmu yasa ka sani, don haka idan bakayi wani abu ba idan aka je lahira kasan amsan da zaka bawa Allah (T) domin mun isar maka cewa, an zalunci Malam Ibrahim Yakoub Al-Zakzaky (H).

An zalunce shi ba boyayyan abu bane don haka hakki ne akan dukkan musulmai su yunkuro su fito, suyi inkarin zaluncin Buhari. Idan wanda ba musulmi bama  zasu fito suce a saki Malam, to ina yake ga kuma wanda yake ga musulmi da yake cewa La'ila ha'illallah Muhammad Rasulallah. Don haka ba yau ne muka soma zagayawa masallatai ba don haka a wannan karo mun iso wannan masallaci, domin ya zamo ma'abota wannan masallacin mu yanke musu Hujja, a kuma sanar dasu halin da Malam yake ciki su san halinda 'yan uwansu musulmai suke ciki, ka tashi  tsaye da addu'a ne! zakayi ko magana ne zakayi !  to duka wannan hakki ne a kanka. Wajibi ne kayi inkarin zalunci, domin yazo a hadisi cewa mutane uku sun yi tarayya a zalunci, da Azzalumi ! da mataimakin azzalumi ! da wanda yaga ana zalunci yayi shiru !! dukansu mataimaka azzalumai ne.

Shehin malamin ya kara da cewa don haka idan kayi shiru muna cewa an zalunci Malam kana cewa ba abinda zaka iya yi kai ba ruwanka, koda addu'a baka yi ba sunan ka azzalumi. Ballantana wanda yake taimakawa Buhari sunan sa azzalumi akan wannan zalunci da yayi. Kuma mu mun fito mu shaidawa Buhari da mukarrabansa dama duniya baki daya America da isra'ila cewa "Ba Gudu Ba Ja Da Baya" wallahi ba zamu bar abinda muke yi na #FreeZakzaky ba a wannan gari sai kun sako Malam. Kuma wannan shine zai zamo cewa Zaman lafiyan ku a wannan gari dama wannan kasa shine ku saki malam domin malam yana bukatan zuwa Asibiti don a duba lafiyansa.

Domin tabbatar da cewa duk fa abinda ya biyo baya ku kuka jawo wa kanku, kuma wanda ya tona ramin mugunta to fa shi zai fada a ciki. Muna sanar da Gwamnatin Buhari azzalumi, Gwamanatin Buhari wanda yake Criminal, Gwamanatin Buhari wanda yake tauye hakkin bayi a wannan kasa muna sanar dasu cewa lallai ba zamu ja da Baya ba akan al'amarin Malam. Dukiyan mu da 'ya'yan mu gaba daya fansane ga rayuwan Malam da mutuncin Malam, don haka akan Malam kada kuyi tsammanin zamuyi sassaucin abinda ya same shi. Don haka zamu fito ba dare ba rana insha Allahu zamu cigaba da gwagwarmaya da fafatawa har sai munga abinda zai kasance na fitowan Malam daga hannun wannan Azzalumai.

Jawabin Shaikh Adamu Tsoho Jos kenan na yau 05/07/2019. a Masallacin Juma'a na FCDA Abuja. Bayan kammala Muzaharar Free Zakzaky.

    --Idishia Jos.

#FreeZakzaky

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post