Gwamnatin Buhari taso Hana Almajiranci ne saboda Kin Musulunci, Domin Su almajirai daliban Qur'ani ne, Yanzu tace ta Haramta Shi'a Saboda kin musulunci da Manzon Allah da iyalan gidansa, Nan gaba kadan zakuji sunce sun Haramta 'yan Dariqa da Qadiriyya, Saboda Tushensu Daya da Shi'a.
🇳🇬MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATES
*Tareda Wakilinmu Muhammad Aliyu Daud (DANSUDAN) Azare 070-32803940*
Wannan abu a fili yake Buhari(L) ya daura ne daga inda Gwamnatin Jonathan ta tsaya, Gwamnatin Jonathan ta cire rubutun Arabbiyya a jikin kudin Najeriya sabida qin Musulunci, wannan kowa yasan da haka.
Yanzu kuma Buhari (L) ya dora daga inda Jonathan ya tsaya ne. Buhari ne yace zai hana saka Hijabi, kowa yaji wannan sannan sunce za su hana Almajiranci duk Sabida qin musulunci, sun hana zagayen Maulidi a wasu guraren sabida qin Manzon Allah sun fake da maganar tsaro, amman sun yi zagayen kamfen dinsu basu ce ba tsaro ba, yanzu ya ce ya hana Shi'a sabida qin musulunci da Manzon Allah da Iyalan gidansa.
Buhari(L) karen farautar Amirka ne da Isra'ila, su ne wadanda basason zaman lafiyar Musulunci da Musulmai, shi kuma yana cika musu muradinsu.
Wai mu qunginya ce, kuma qungiyar 'yan ta'adda! Wannan qaryar har ina kowa yasan cewa ba'a taba samun 'yan Shi'a da ta'addanci ba a tarihin duniya gaba daya, sai dai a yi musu ta'addancin, in kuma a kwai mutum ya fada mana.
Wannan ba boyayyen abu ba ne, daman mu Musulmai sunanmu 'yan ta'adda a wajen maqiya Musulunci, wannan ba su boye ba sun fada sun kuma nanata, duk wani alamin musulunci shine ta'addanci a wajensu.
Daga sun yi maganar ta'addanci sukan siffanta Musulmai ne.
Gwamnatin da bata bin Umarnin Kotu ne, za ta fake da Kotu don ci gaba da ta'addancin da take yi. Wanda kowa Shaida ne tunda ta hau mulki take kashe Musulmai, Mutane basu dauke da makami suna qiran sunan Allah, suna cewa Allahu Akbar amman tsabar qin musulunci Gwamnati take kashe su!
Yanzu ta fake da kotu shin ba tasan da Kotu ba ne take kashe su ba tare da ta kai su kotu don hukunci ba, sai yanzu tsabar renin wayo, da son wawintar da hankalin gafalallu. Don tanason buda kisan nata na zalunci zuwa ko'ina,
Ba ki bi Umarnin kotu ba, amman wai za ki fake da kotu don son cigaba da zubar da jinin bayin Allah.
Toh ki shina Mu bazamu taba barin musulunci ba, abinda muke musulunci muke, mu ba qungiya ba ne, mu Musulmai ne, baza mu taba dena abinda Musulunci ya ce mu yi ba.
Da Allah muka dogara kuma shine mai bamu kariya.
*Kakaninku sun haramta Musulunci a Makka zamanin Manzon Allah kuma Allah ya daukaka Musulunci a gaban idanun maqiya Musuluncin, Kuma abinda zai faru kenan a wannan qasa Wallahi musulunci sai ya tabbata a wannan qasa, sai ya yi iko da wannan qasa, da kunqi da kunso.*
*Manzon Allah da Iyalan Gidansa haskensu sai ya haskaka ya game gidan kowa a qasarnan, Fahimtar waye Manzon Allah da Iyalan gidansa ya zo kenan ba komawa sai dai ku yi duk abinda za ku yi.*
Ina dai kisa ne ko kamu toh wallahi akan Annabi da Iyalan gidansa, akan Musulunci mun yadda ku yi mana komi, in kuna da Jahannama ku sakamu, in kunajin kuna da Aljannah ne bamu buqata.
Sabida Jahannamarku bata kai ta Allah ba, Aljannarku bata kai ta Allah bah. Duka ku riqe kayanku bama so.
Mun yadda ku mana komi in mutuwa ce in kun kashemu munyi shahada, in kun tsaremu halwa da kuma qara samun yaqini da daukaka duniya da lahira.
Baza ku taba kashemu ba in lokacinmu bai yi ba, Hakama baku isa ku yi mana wani abu ba wanda Allah bai qaddara mana shi ba.
*Har abada baku isa ku shafe ambaton Manzon Allah da Iyalan gidansa ba, ba ku isa ku shafe musulunci ba, Hakama baku isa ku shafe ambaton Sayyid Zakzaky(H) ba, Allah ne ya tada shi*
Baku isa ku qarar damu ba, za ku iya yin kisa bance baza ku iya ba, amman mune da nasara, ku duba tarihi da kisa da kamu na maganin Shi'a da bata zo garemu ba, da kisa da kamu na hana musulunci da yanzu ba Musulunci
Mu madogararmu Allah ne, ku kuma madogararku Shedan ne, toh mu zuba mu gani mu daku, shege ka fasa.
Yan'uwa mu tuna da wa'yannan Ayoyin Kamar haka:-
Allah ya ce "Qul'amantu billahi summastaqim"
Fassara "Kace ka yi Imani da Allah, sannan ka tsaya ka dake".
Mu tsaya mu dake ba gudu ba ja da baya, muke da nasara. Komi za su yi sai dai su yi.
Allah ya ce " Waman yata wakkal Alallahi Fahuwa hasbuh" Fassara duk wanda ya dogara ga Allah, toh Allah ya isar masa"
Mu mun dogara ga Allah ne, kuma ya isar mana bazamu tabajin tsoron wani ba, ko wani abu bakin bindiga ba.
Allah yace "Wal aqibatu lil muttaqin" Fassara qashen Al'amari (Nasara) na masu tsoron Allah ne.
Mu jure nasara tamu ce, qarshen lamarin na garemu.
Allah yace "In tansurullaha yansurukum wa yu sabbit aqdamakum" Fassara In kun temaki Allah, Allah zai temake ku, kuma ya tabbatar da dugaduganku"
Gwamnati tana gaba da musulunci ne, in muka dake Allah zai tabbar da dugaduganmu.
Allah ya ce " Yuriduna Li yud'fi'u nurallahi bi afwa hihim wallahu mutimmu nurihi walau karihal kafirun"
Fassara "Suna so su bice hasken Allah ne da bakunan su, Allah kuma zai cika haskensa koda kafirai sunqi"
Tabbas koda Amirka da Isra'ila da yan korensu, basason hasken Allah ya cika na tabbatar musulunci a wannan qasa, toh Allah yai alqawarin cika alqawarinsa koda basaso. Addini insha Allah kamar ya yi iko ne da wannan qasa.
Wannan abinda da kuke, shi yake qara kusanto da faruwar hakan a kusa-kusa. Kuci gaba da abinda kuke mu hakan nasara ne a garemu.
Allah ya ce " Wa ukra tuhibbunaha nasarun minallahi wa fatahun qarib"
Fassara "Da wata falala da yake kuna sonta: taimako daga Allah da cin nasara wanda yake kusa. Kuma ka yi bushara ga muminai"
Ku yi komi nasara tamu ce da temako daga Allah kuma gareshi muka dogara. Allah ya na tare damu kuma ya yi wa muminai bushara.
Allah ya ce " Ya ayyuhallazina amanu kunu Ansarullahi, kama qala Isah bin Maryama Lil Hauwariyyina man Ansari illallah..."
Fassara "Ya ku wadanda su ka yi Imani! Ku kasance mataimaka Allah, kamar yadda Isah bin Maryama ya ce ga Hawariyawa, su wane ne mataimakana zuwa ga Addinin Allah!?".
Yanzu mu Sayyid Zakzaky(H) ya ce damu su wanene mataimakansa, zuwa ga aikin Allah. Mu tsaya mu dake mu zama mataimakansa na gaskiya.
'Yan'uwa abinda ya hau kanmu shi ne, mu gyara tsakaninmu da Allah, da sauran Al'ummah da kowa da kowa dangi da Amawa.
Mu tuba ga zunubammu, mu qara tsayuwa da Addini lokaci, ya yi kada a tankade da kai, ka yi asarar duniya da lahira.
*FREE ZAKZAKY WA UMMUNA ZEENAH DOLE*
*DANSUDAN AZARE 070-32803940*
Tags:
Tunatarwa