-Sheikh Adamu Tsoho Jos
Muna wannan fitowa ne sabida halinda jagoranmu Sheikh Zakzaky yake ciki, wanda wannan azzalumar hukuma na Buhari yau kusan shekaru hudu kenan bayan sun kashe darurukan Almajiransa shima sun kashe 'ya'yansa, shima suka harbeshi kuma yanzu haka yana tare da raunuka kuma suke shayar dashi Guba. A tsawon wannan lokaci wannan azzaluman hukuma na Buhari tana rike dashi bayan kotu tace a sake shi bai yi laifin komai ba har ma a biyashi diyya. Don haka muna fitowa mu nunawa duniya irin zaluncin da ake yiwa almajiransa da irin abinda ake wa sauran musulmai baki daya.
Domin da yawa wasu na cewa wannan bai abin bai shafesu ba, to lallai ya shafe su, domin idan aka yi zalunci a boye baka sani ba to wannan bai shafeka ba, amma idan zalunci ya bayyama aka ce ga zalunci ana aiwatarwa, to ya zama hakki akan ka na musulmi mai shaidawa da La'ilaha illallah Muhammad Rasulallah ! Ya zamo kayi inkarin wannan zalunci. Idan zaka iya kayi inkarin sa da hannun ka, idan ba zaka iya ba kayi inkarinsa da bakin ka, idan ba zaka iya da bakin ka ba kayi inkari da zuciyarka. Wannan shine af'aful iman wanda mutum zai iya tsayawa dashi.
To muna fitowa domin mu nuna wa al'umman musulmai cewa irin zaluncin da Gwamnati Buhari ta aiwatar na kisan kiyashi da suka yi sannan kuma basu gushe ba suna rike da Malam. Sannan wannan fitowan namu idan akan malam ne ba gudu ba ja da baya, ba zamu gushe ba muna fitowa mu na shaida bara'a din mu ga wadan nan azzaluman mahukunta na wannan kasa da magoya bayansu na kasashen duniya Amerika ! Isra'ila da Saudi Arebiya. To su sani cewa wannan da'awa ta Malam nan gani nan bari domin abu ne na Allah (T) da ya dasa kuma yakai kusan shekaru arba'in da malam yake kira akai.
Wannan da'awa ce da take kira ga La'ilaha illallah Muhammad Rasulallah (S), da'awa ce wacce bata banbanta dan wannan Kungiya da dan wannan Kungiya in dai ka amsa sunan ka na musulmi to wannan da'awa tana magana da kai ne. Allah ya aiko mana da Manzo Muhammad ya Isar mana wannan sako kuma ya isar da wannan sako wanda yake a kunshe a cikin Alkur'ani, kuma Alkur'ani an aiko mana dashi ne don muyi hukunci dashi, kuma mun samu kammu ne a cikin wannan kasa wanda ba ana hukunci bane da Alkur'ani akan wannan malam ya tashi ya tsaya yana fadakar da al'umma cewa a matsayin mu na musulmi ba muda wani uziri in mun koma ga Allah in har bamuyi hukunci da Alkur'ani ba.
Akan wannan ne Amerika da Isra'ila da hadin bakin Saudi Arebiya suka dauki wannan mataki domin su kawar da Malam daga doron kasa. Wanda ya kai ga wannan wakiya an kashe darurukan almajiran Malam. Har a wannan sati zamu iya cewa tun daga ranar Litinin har izuwa talata almajiran malam basu gushe ba ana musu barazana a Abuja da Kaduna, wanda har an kashe mutane a Abuja da Kaduna akan fitowa ana Muzaharar FreeZakzaky ! To muna anan bamu gushe ba muna cewa FreeZakzaky. Kuma abinda Zakzaky yake fada muke kai a kai idan yace La'ilaha illallah Muhammad Rasulallah (S), idan yace azo abi Allah da Alkur'ani laifi ne to muma duka munyi wannan laifi din, dukkan mu muma Zakzaky ne idan kuna da makamai kunsan gidajen mu.
Akan wannan da'awa ku sani ba zamu ja da baya ba, zamu cigaba da fadakar da al'umma halinda ake ciki da kuma munakisa da makirci na ainihin kasashen waje suke kullawa akan wannan al'umma. Wanda malam yayi magana akan Zamfara mutane basu gane ba, sai da abinda yake faruwa a Zamfara yanzu sannan mutane suka gane. To wannan yana daga cikin abubuwan da su Malam yake tona asiri manya-manyan kasahen duniya wanda yake suke manaye sauran kasahe. Don haka ya zamo yau ma min fito mun shelantawa duniya kamar yadda sauran al'umma suke fitowa su shelenta cewa Buhari FreeZakzaky ! Wannan shine da'awan idan Buhari bai saki Malam ba to ya sani cewa duk wani Abu da ya biyo baya shi ya jawa kanshi.
Ba zamu gushe ba muna daukan matakai daban-daban domin ganin cewa su Malam sun fito, malam yana cikin yanayi na tsananin rashin lafiya, wanda likitoci sun zo sun tabbatar dashi da iyalinsa an harbesu da harshashi mai guba sannan kuma an sa musu guba a cikin abinci wanda ya zamo yanzu giban nab yana hawa jikinsa. To ku sani cewa ba zamu taba yarda da wannan al'amari ba, kuma duk abinda ya samu malam Buhari ne zamu kama da ainihin Gwamnan Kaduna dan tatsitsi Nasiru ElRufa'i. Don haka wannan sanarwane sannan muna isar musu da sako da wannan sako namu.
Jawabin Shaikh Adamu Tsoho Jos kenan na jiya 13/07/2019. a Masallacin Juma'a na na garin Jos. A lokacin gangamin FreeZakzaky da akayi a masallacin.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates.
--Idishia Jos.
#FreeZakzaky

Tags:
#FREE_ZAKZAKY