Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates, Tare da Wakilinsu -Idishia Jos.
An gudanar da Sallahr Jana'izar Shahid Ahmad Nasir wanda akayi a Babban Masallacin Juma'a na maraban jos, Shahid Ahmad Nasir ya samu wannan tagomashin na rabauta da Shahada ne a jiya Alhamis 11/7/2019 wajen nemawa jagora 'yanci watoum Muzaharar #FreeZakzaky wacce akayi da ranar jiya alhamis a Jahar Kaduna, inda anan ne karnukan jami'an tsaron 'yan sandan Najeriya suka budewa masu muzaharar lumanar wuta, anan ne Allah Ta'ala ya azurta Shahid Ahmad Nasir da samun Shahada, inda da Safiyar yau juma'a 12/7/2019 akayi masa Sallar Jana'iza a Babban Masallacin Juma'a Maraban Jos.
Assalamu Alaika ya Shahid Ahmad Nasir Ranar da aka haifeka da ranar da aka kasheka da ranar da za a tasheka a matsayin wanda aka zalunta.
Allahumma Swalli Ala Muhammad Wa Ahli Muhammad Hadiya ga ruhinka tsarkakakke.
Ga wasu daga cikin hotunan jana'izar
Tags:
Labaran Duniya