Sheikh Zakzaky tare da Malama Zeenat a lokacin da suka iso Kotu a Kaduna. |
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates, Tare da --Idishia Jos.
Babban Kotu a Kaduna ta dage sauraron shari'ar da aka yi yau, na Jagoran Harkan musulunci Sheikh Zakzaky. Bayan an jira babban Lauyan nan Femi Falana ya iso kotu kafin aka fara sauraron shari'ar. A lokacin da aka glauyoyi suka gabatar da kansu a gaban kotu, an fara sauraren shari'an ne kamar yadda aka saba. Lauya mai kare Sheikh Zakzaky Femi Falana (SAN) yayi nuni da neman izinin Kotu da a gaggauta sakin sheikh Zakzaky don yaje yayi jin a kasar Indiya.
Lauyan Gwamnati Bayero Dari ya shaidawa kotu cewa wadanka ake kara suna wajen kotu. Saboda ba sa iya hawa gidan sama. Shima Falana ya ce rashin lafiyar da suke fama da ita ba za su iya hawa sama ba. Lauyan Gwamnati ya kara da cewa yau da safe ne lauyoyin wadanda ake kara suka basu amsa a rubuce kuma takardar na da shafuka kusan ashirin da wani abu. Sai alkali ya ce masa bai kai haka ba. Bayero ya ce ya hada lissafi ne duk da medical report. Don haka ya nemi kotu ta basu dama don amsawa a rubuce.
Motar da aka kawo su Malam Kotu a yau. |
Falana ya nuna rashin amincewarsa. Ya ce jiya ne lauyoyin gwamnati suka basu amsar application dinsu na farko. Amma har su lauyoyin Sayyid sun yi nazari sun basu amsa daga jiya zuwa yau. Don haka ya ce ba so yaje ya yi jayayya kan wannan bukata ta lauyoyin Gwamnati ba, amma idan aka yi la'akari da halin da wadanda ake kara suke ciki dole a gaggauta daukar mataki. Ya ce a makon da ya gabata Malamin ya sami shanyewar bangaren jiki na dan wani lokaci. Sannan yau kwana 7 bai sami yin bacci ba duk da alluran baccin da aka yi masa. Don haka ya roki kotu da ta yi watsi da wannan bukata da Bayero.
Daga Karshe Lauya Gwamnati Bayero ya ce abin da yake son fadi a rubuce yana da muhimmanci saboda haka ya roki kotu da a bashi kwana 7. Nan kuwa Lauyan da yake kare su Malam yace ya aminta da haka, kuma kotu ta yarda da cewa sai nan da mako daya za'a dawo a cigaba da sauraron shari'ar. Duk da yake Sheikh Zakzaky da mai dakinsa basu iya shiga cikin kotun ba saboda rashin lafiya da yake damunsu.
#FreeZakzaky
Tags:
Yanar gizo