An bayyana Shaikh Yakubu Yahaya Katsina a Matsayin Masanin Tarihi da iya bada Darussa da shi

Wani Kirista daga Majami'ar Catholic ne ya bayyana haka a Yau Asabar alokacin da yake maida Jawabi a wani taron tunawa da Zagayowan watan Haihuwar Annabi (A.s) na watan Kamariyya wanda Matasan Harkar Musulunci Karkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Alzakzaky ke shiryawa Kiristoci duk shekara a Katsina.

Mr. Chijiok John ya bayyana cewa,gaskiya su Kiristoci kam suna jin dadi matuka akan yadda ake shirya masu wannan Muhimmin taron Murna da Zagayowan watan haihuwar Yesu Almasihu na watan Musulunci,wanda hakan wani bangare ne na yaukaka zumunci da zamantakewaa tsakanin juna.

Mr. John ya kara da cewa; "A gaskiya muna jin dadin wannan 'Program' da kuke shirya mana,shiyasa 'Always' muke halartansa."

Da yake nuna gamsuwarsa akan Jawabin da Mai Jawabi ya gabatar a taron da ya kumshi tsantsan Tarihin Annabi Isa(A.s) da darussan da ke a ckumsha a cikin rayuwar tasa,Kiristan yace, Akasarin Malamai ba suna Fassara tarihin kamar yadda shi Malamin yake fassarawa Mutane  ba.

Har wayau,Mr. Chijiok John ya kuma yabawa Almajiran Shaikh Zakzaky dangane da yadda aiwatar da harkokinsu cikin tsari da iya Kyakkyawar Mu'amala dasu,sannan ya kuma jinjina masu akan yadda suke halartar wasu Sabogogi nasu idan sun gayyace su inda ya nuna hakan a matsayin rashin kyamar A'umma,ya kuma yi kira ga sauran Musulmi da cewa su yi koyi da irin wadannan Halayen nasu.

Tun farko da yake gabatar da Jawabi a taron,Shaikh Yakubu Yahaya Katsina yayi bayani tiryan-tiryan wa Kiristocin akan Tarihin Annabi Isa (A.s), zamantakewa a tsakanin Musulmi da Kiristoci,da kuma yadda za suyi maganin makirce-makircen makiyansu akan kokarin haddasasu rashin jituwa a tsakanin junansu.

Malam Yakubu Yahaya dai yasha samun irin wadannan Lambobin yabo na Sanin Tarihi daga Masana Ilimoma daban-daban,ko a shekarar da ta gabata Farfesa Dahiru Yahaya daga Jami'ar Ahmadu Bello Zariya ya bayyana Malamin a Matsayin wani jigo na samar da Tarihin Jahar Katsina.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post