Jami'an tsaron Nigeriya sun sake afkawa masu Muzaharar Lumana a garin Abuja,a lokacin da ake kira da gwamnatin Nigeriya data gaggauta sakin Jagoranmu Sayyid Zakzaky. Muzaharar wanda aka fara a Federal Secretariat a nan garin Abuja. Sun harbi mutane da daman gaske ciki harda yara da mata.
A yayin da suke Muzaharar kin amincewa da shayar da Sheikh Zakzaky Guba a inda yake tsare tare da nuna rashin amincewan mu da cigaba da tsare shi tare da iyalinsa. A yanzu haka wasu kafafen sada zumunta na Internet sun fara yada cewa muna kone-kone a cikin Abuja, to muna nisanta kammu da wannan ta'addanci da suke jingina mana.
A yanzu haka sun harbi mutane masu yawa kuma sun shahadantar da mutum daya.
Daga shafin Ma'asumah Nigerian News Updates, Tare da -Idishia Jos.
Ga wasu daga cikin hotunan wakiyan
#FreeZakzaky.
Tags:
#FREE_ZAKZAKY