-Sheikh Yakubu Yahya Katsina.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates, Tare da --Idishia Jos.
Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, dalilin fitowan mu musamman yau da aka kai su Malam Kotu, kuma sukayi abinda suka ga dama wanda ya sabama dukkan dokoki na duniya dana hankali dana ilimi da ka'ida da doka. Ko ba komai bawan Allah kowa yasan halinda yake ciki na Guba da aka bashi, wanda kuma duk duniya ta shaida, koda mutum kisan kai yayi sai ya zamo baida lafiya ko gobe za'a rataye shi sai an kai shi asibiti ya samu lafiya sannan azo a rataye shi. Ballan tana Malamin nan ba abinda yayi ko ya taka ya zubar na wani, Malamin nan yana bidan Rahma ga al'umma, Malamin nan yana son kasan nan ta zauna cikin aminci.
Ba yadda za'ayi ace mutumin da ke da mabiya irin wannan miliyoyi daban-daban da matasa majiya karfi, wanda linzaminsu yake hannun addini wanda da ace wannan lizamin ba a hannun addini yake ba, da wannan matasa da ba linzamin su a hannun addini yake ba a wannan yanayi da malam yake ciki ba wani labari ake yi daban. Ya kamata wannan Malami a yaba mishi yadda ya tarbiyantar da wannan masu jini a jika, ya samu su hadafi da manufa wanda suke hange ta nan gaba ba tanan kusa ba, ya sa musu tunani da kwakwalwa na hangen nesa, wato hangen inda ake so aje. Da badon haka nan ba da Yanzu wannan mutanen ko ance suyi abinda suke yi ba zasu yi ba.
Saboda a cikin matansan akwai wanda in zasu ga mutuwa da ido da zasu rungumeta. Amma kuma wannan abin ba'a ganinsa sam, bama mu ba akwai wani babban mai shari'a yace "Activision" guda bakawai suka bugo mishi waya suna cewa yaushe za'a yi shari'a yace ku taimaka ku saki Malamin nan, "Activision" manyan malaman Kiristoci guda bakwai. Akwai wasu tawaga kuma da suka je suka samu mai yin asalin shari'a din wanda ya tafi aikin zabe Tawagan Kiristoci sun Je sun same shi, suna cewa ku taimaka ku saki wannan bawan Allah, wannan bawan Allah shine zaman lafiyan kasan nan. Ku sake shi, banda kiraye-kirayen kasashen waje, banda kiyare-kiraye daga majalisan kasa, banda kiraye-kiraye daga manyan malamai masu mutunci irin su Shehu Dahiru Bauchi, Shenu Abduljabar da makamantansu banda masu hankali wanda suke ganin abinda zai je ya zo.
Suna ganin hatsarin da ake fuskanta, amma mutanennan sun yi shiru saboda me ! Suna da wani hadafi da suke son su cimmawa. Sannan sun nuna yaudara sabida sun yiwa su malam "Visa" da passport da komai an musu wanda da bassuda su duk an ma su malam wannan da inda aka ayyana sannan daga baya ace ba za'aje ba, wannan yaudarace da cin amana don haka ba zamu yarda dasu ba. Wato sun fi son a cigaba da jinane a cigaba da kashe rayuka, to shikke nan duk jinanen da ke zuba da rayukan da ake rasawa jarine a cikin wannan tafiya din. Domin addinin musulunci in baku sani ba yana kafuwa ne da jinane da kuma sadaukar da rayuka. Domin dan abinda ya faru kwanakin nan yasa duniya yanzu ta farka sakamakon wannan jinanen da aka zubar, an zubar da Jamal nanen mutane mutane kuma sun farka a duk duniya.
Kuna haka ma kanku ramin da zaku binne kanku da kanku, sannan kuma wannan muzaharar da muka fito ba fada muka yi a gidajen radio ba wani yaji ga wane za'ayi ne amma Ku duba mutanen da suka fito suka zo wannan wajen. Akwai wata kungiya wai kunyan masu kin zalunci suna gangami cewa zasu fara muzahararori na ba ji ba gani duk wani wanda yake kishi ya shigo ayi tare dashi. Wannan bamu san wannan kungiya ba amma Yanzu gashi ta bayyana, 'yan Nigeria ne 'yan kishin kasa ne wanda basa son ayi zalunci. Da bamu san dasu ba amma Yanzu abinda kukewa malam ya fito da wannan mutane to an dinga kenan Kiristoci da Musulmai da sauran masu imani sun dinga fitowa kenan har abin ya kai yafi karfin ku ya kwace muku, kuma duk abinda kuke yi inda Allah ba zaku kai mu ga bango ba domin mu addini muke, ba kuma zamuyi sabanin addinin mu ba.
Kadan daga Jawabin Sheikh Yakubu Yahya Katsina wanda yayi jiya da dare bayan kammala Muzaharar kin yarda da tsare Sheikh Zakzaky da ake ba tare da an fitar dashi waje don kula da lafiyansa ba.
--Idishia Jos.
#FreeZakzaky.

Sheikh Yakububyahya a lokacin da yake jawabi |
Kadan daga Jawabin Sheikh Yakubu Yahya Katsina wanda yayi jiya da dare bayan kammala Muzaharar kin yarda da tsare Sheikh Zakzaky da ake ba tare da an fitar dashi waje don kula da lafiyansa ba.
--Idishia Jos.
#FreeZakzaky.
Tags:
#FREE_ZAKZAKY