ADDININ MUSULUNCI YA SHAFI DUK RAYUWA NE!
Nigeria ina Mafita Na Sheikh Zakzaky
Ishaq Muh'd SuleimanƘa'idoji da dokokin sun haɗa da halin rayuwar mu a kullum, kamar wurin kwanan mu da suturar mu, da abincin mu, duk akwai dokokin Allah aciki, kai hatta ma hulɗa a tsakanin yamu yamu kamar ciniki da sana'o'i duk akwai ƙa'idojin Addini aciki,
Saboda haka Addinin Musulunci akwai nasa fagen, wanda yake Alƙur'ani ya ƙaryata cewa Addini ya shafi dangantakar mutum da Ubangijinsa ne kawai ta fuskancin Addu'o'i da sadakoki. Don in muka duba Ayoyi da hadisan Manzon Allah (S) suna magana kan abinda ya shafi rayuwa gaba ɗaya ne, saboda haka magana akan wannan, wani abu ne daya shafi Addinin Musulunci gaba ɗaya. Muna iya ganin cewa a cikin shika-shikan musulunci akwai Sallah da Zakka, kuma sau da yawa Allah yana gwama Sallah da Zakka a wurare daban-daban, "ku tsaida Sallah ku bada Zakka"
Sallah alamin Ibada ne wadda take tsani tsakanin bawa da Ubangijinsa, wanda yake ita Sallah itace babba daga cikin waɗannan Ibadodi, Zakka kuma tana alamin adala (adalci) da ke tsakanin waɗanda ke zaune a wuri guda, tunda akan karɓi wani abu dake tsakanin masu shi zuwa ga hannun marassa shi, domin kar ya zama wasu sun tafi Hazzozi wasu kuma sun rasa.
Kuma yazo a cikin Alƙur'ani, "Allah Ta'ala yana cewa: Da Allah zai buɗe ƙofar Arziki a duniya, da mutane sunyi Shishshigi abayan ƙasa, amma yana saukarwa daidai gwargwado ne ta yadda yaga dama" wato Shishshigi anan shine Allah Ta'ala ya Azurta kowa, to da wasu kila bayan gidansu da burodi zasu share saboda wadata (maimakon takarda) sai a nemi burodi a share saboda Shishshigi, ko kuma inda ze zauna se yayi na zinariya,
Amma muna iya ganin Azzalumai waɗanda sukayi Shishshigi, inda ma zasuyi bayan gida se Anyi musu na zinariya, ko kuma inda zasu ɗora ƙafafuwansu akan kujera, sai ayi na zinare, da ace Allah ya yalwata arziƙi, wato zinari da azurfa su wadata, da Ɗan Adam yayi Shishshigi, da bai ga Darajar abinda aka bashi ba. To amma shi Allah yana saukar dashi daidai gwargwado, bai yi yawan gaske da zai kai su ga ɗagawa ba, bai kuma ƙaranta ƙwarai yadda zai kai su ga shiga wani matsanancin hali ba.
Idan har ya zamana cikin abinda Allah yake saukarwa ɗin nan, domin su sami abinda zasu tsaya da rayuwarsu ta yau da kullum ya zama ya gagara, sun rasa, to wasu ne suka ƙwace musu nasu haƙƙin, tunda Allah Ta'ala yana saukar da daidai gwargwado. In kaga wasu basu da shi, to wasu masu shine suka ƙwace haƙƙin wasu, tunda an saukar dashi ne daidai gwargwadon buƙatun (kowa)
To kuma zamu ga cewa Allah sau da yawa ya yalwata arziƙi da cewa wani abu ne daga gareshi, dama Allah shi ke saukar da ruwa daga gareshi, shi ke kuma tsirar da tsiro ne dake tsirowa daga ƙasa, da kuma dabbobi da muke hawa, su sha ruwa, suci Abinci, kazalika ma ya bizne a ƙasa, shi ya bizne ƙarfe da zinare da azurfa, shi ya bizne Mai da Gwal da Kuza, da kuma dukkanin nau'o'in arziƙi da suke bizne a ƙasa, kuma Allah shine ya halicci ruwa da halittun da ke cikin ruwa, duk arzikin da ya taru cikin ruwa Shine yayi wannan,
Saboda haka shi ke Azurta mutane, tushen arziki shi ne, don haka kamar yadda Allah Ta'ala yace Al'amarinsa ba halitta ne kurum ba.
Tags:
Taskar ilimi