YUNQURIN KASHE SHAIKH ZAKZAKY A MULKIN JONATHAN:



__Da yake a lokacin ‘Yar’adua a shekarar 2009 sun qirqiri wata qungiyar ta’addanci da ‘yan gidan Rediyo suka saka mata suna Boko Haram, wanda daga baya aikin ‘yan qungiyar ya zama shine kai hare-haren bama-bamai a masallatai, cocina da kasuwanni, kuma duk da sunan wai suna yunqurin kaf addinin Musulunci.
Shaikh Ibraheem Zakzaky ne kadai Malamin da tun farkon fara wannan ta’addancin da suka kira Boko Haram, ya yi tsayin￾daka wajen wayar da kan al’ummar Musulmi kan cewa an qirqiri wannan qungiyar ne saboda fada da Musulunci.
A ranar 6 ga watan Augustan 2009, a yayin da yake jawabi a wajen bikin Nisfu Sha’aban, a Fudiyyah Islamic
Center, Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa:
“In nai shiru ban ce muku komai ba dangane da Boko Haram za ku ce to ai yanzu muna fuskantar matsalar tsaro ne ya mamaye mu. Wannan yana daga cikin dasisa da suka qirqiro shi domin su mai da da’awar Musulunci wani mummunan abu. Su suka qirqiro wannan abin da suke fada da shi din, suka je kuma wai suna murqushe shi. To da suka je murqushewan nan, sai suka hada da duk alamin Musulmi. Yanzu gemu Boko Haram ne, doguwar jallabiya Boko Haram ne, hijabi Boko Haram ne, kuma an riqa dambarawa mutane harsashi (alhali ba su ji ba, ba su gani ba) a cikin Maiduguri. Har ta kai ma ga an ce min wadansu Sojoji da aka kai birnin Maiduguri suna bindige kowa ne, hatta dan sanda, sai da ya je yana cewa mutane ku shige gida sojoji aka turo, kowa suke harbewa. Kawai kowa aka gani dambara masa harsashi ake yi. Amma duk duniya mu an ce mana wai wadansu mutane ne suka bayyana wai sunansu wai Boko Haram. To, ba wani Boko Haram! Fada da Musulunci ne! Cikin abubuwan da suke yi har da kware hijabin mata. To hijabi shi ma laifi ne? Ba addinin Musulunci ne ya ce a yi Hijabi ba, da nassin Alqur’ani, to me ya sa ya zama mummunan abu? Gemu ba alamin addini ba ne?Na’am. Sun qirqiri wani mutum wanda sukai amfani da shi, don su fake da wannan, kuma suna da wata manufa; La’alla daya daga cikin manufar shi ne akwai Mai shimfide a Borno da Yobe da Gombe da Bauchi, wadannan jihohi hudun, duk jihohin Mai ne. America tana so ta zo ta debi Man, (kuma ita) ba ta zuwa ta debi Mai sai ta haddasa rikici. Duk inda za ta debi dukiya sai ta haddasa rikici.
________________________
Ma'asuma Nigerian News Update.
__Yunkurin kashe sheikh Zakzaky ashekaru goma__
Tareda wakilinmu;
©___Mahadi Tukur Almizan.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post