YANZU MUNA MARHALIN JARABAWA NE

     -Sheikh Adamu Tsoho Jos

A wannan lokacin da muke ciki muna cikin marhalan Jarrabawa, jarrabawa babba ga dukkan wani dan harka islamiyya a wannan kasa da ma kasashen duniya, domin Malam da'awansa ba kawai ta tsaya a wannan kasa bane, ba'a Africa bane da'awace wacce take alamiyya ta Duniya. Don haka a irin wannan jarrabawa da bamu taba fuskantar shi ba, duk da yake anyi jarrabawa a baya daban-daban to amma wannan jarrabawa tazo da wani salo tazo da karfi fiye da sauran jarabawowin da suka gabata basu zo da wannan karfin ba.
-Sheikh adamu tsoho jos


Allah ya kan jarraba mabiya Malam ne amma wannan jarrabawa da tazo! Tazo ne da manufar kawar da Malam daga doron kasa da kawar da Harka daga doron kasa a aikace ne suka gabatar, sun dauki dukkan matakai ne da zasu kawar da Malam wanda kuma mun gani da matakai na kawar da Harka da matakai na kawar da Almajiran Malam munga abin da ya gudana a wakiya din nan. Darurukan Almajiran Malam Maza da Mata Manya da Kanana harda tsofaffi wadansu ma da ransu aka kona su da wuta, wasu kuma da ransu aka binne su.

Wannan azzaluman Gwamnati karkashin Shugaban kasa marar rabo Buhari da Kwamandan Sojojinsa suka je har gidan Malam bayan sun kashe darurukan Almajiransa, suka kashe 'Ya'yansa suka kashe Yayarsa, shima kansa Malam din da Iyalansa suka kashe su, amma kamar yadda muke bayani Allah (T) sai ya nuna iko na cewa mutuwa da rayuwa ba a gun kowa yake ba yana hannun Allah ne. Don haka Allah ya hukunta Malam yana da sauran rayuwa shiyasa har yanzu suna nan cikin ludufin Allah, Ubangiji ya nuna musu wannan manufa na goyon bayan Amerika, Isra'ila da Saudi-Arebiya ya zamo basu iya cimma wannan manufarba. 

Malam dai yana nan har yanzu duk da yake yana tare da raunuka da harshashai, kamar yadda Iyalansa ma tana fama da jikinsu, amma dai Alhamdulillah ana ziyarsu ana kuma ana ganin su akan ji daga garesu da makamantansu. To haka kuma Harka wanda akan Harkane suke son kawar da su Malam to itama tana nan daram ba zasu iya kawar da ita ba, bil hassani ma sun kara kaimi ne ga su 'ya'yan harka din. Tunda gashi nan muna nan abinda ake yi ba'a fasa ba, kuma wasiyanda su Malam suka yi a cika gaba da komai ana nan a na cigaba ba tare da wani mishkila ba.

Kadan daga cikin jawabin Sheikh Adamu Tsoho Jos wanda yayi ranar 8 ga watan Shawwal 1440Ah wanda kuma yayi daidai da 10 July 2019, a lokacin ziyarar goron Sallah da 'Yan media Suka kai masa.

    --Idishia Jos. 

#FreeZakzaky
@Media Forum Jos.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post