_WANNAN SHI NE JAWABIN SHEIKH IBRAHIM ZAKZAKY A LOKACIN YANA MATAIMAKIN SHUGABAN KUNGIYAR DALIBAI MUSULMI A NIGERIA_________
Da sunan Allah mai murkushe azzalumai.
_________
Ya ’Yan uwa Musulmi maza da mata! Assalamu alaikum wa rahamatullah. An
ruwaito cewa Sayyidina Ali Dan Abu Talib
(A.s) yace Manzon Allah (S) ya ce; ‘idan wani ya ga wata gwamnati ta mai
da zalunci kiranta, ta keta haddodin Allah,
ta shuka kiyayya ga sunnar Manzon Allah,
tana aikata barna da zalunci a tsakanin
bayin Allah,
to a wannan hali duk wani wanda bai yi amfani da hannunsa da
bakinsa ya yi yaki da wannan zalunci da
barna ba, to ya sani fa Allah zai kai shi
matsugunin wannan Jagoran gwamnati,
ya sa duk cikar su a wuta.”
To fa! Ga shi kuwa gwamnatin kasar nan
ba ma kawai ta mai da zalunci kiranta
bane, a kan zalunci ne aka gina ta; ba ma
kawai ta keta haddin shari’ar Allah bane,
ta aje shari’a ne waje guda ta dauki
shari’ar da mutum ya tsara; ba ma kawai ta karya alkawarin Allah bane, tun farko
ma ba ta dauki alkawarin Allah din ba!
Ta ki ta dau alkawarin Allah, ta yi wa Allah
tawaye, amma ta dauki alkawarin Dagutu.
Ba ma kawai tana aikata barna da zalunci
a tsakanin mu bane, ai ta ma mai da
wannan zalunci adalci! Ba shakka mu kuma ba ma kawai mun ki
yin amfani da hannuwanmu da
bakunanmu don mu yaki wannan zalunci
da barna bane, ai mune da kanmu muka
yarda ta aikata wannan barna da zalunci
a kanmu!
Mune fa muka zabi wannan azzalumar gwamnati da hannuwanmu,
kuma muke goyon bayanta da
bakunanmu. Kun ga ashe mune muka ba
shugabannin gwamnati damar su zalunce
mu, su kau da shari’ar Allah waje guda, su
dauki shari’ar da mutum ya tsara. Mune muka ba su damar su aikata barna
da zalunci a tsakaninmu,
kuma su mai da
wannan barna da zalunci halal. Ba ma
kawai mun ki yin amfani da jikinmu da
bakinmu don mu yaki wannan hali bane, a
maimakon haka, mu ke karfafa musu gwiwa su ci gaba. To fa ’yan uwa Musulmi! Idan wannan
hadisi ya ce duk wanda ya ga wani
shugaba yana zalunci, amma ya ki ya
yake shi da ayyukansa da bakinsa, to ya
sani fa makomarsa daya da wannan
azzalumin Shugaban,
to ina ga mu? Kun ga ashe ba ma kawai yana ga Allah na ya
dauke mu Ya kai mu mazaunin wadannan
azzalumai, Ya sa dukkanmu a wuta ba, ai
mu da kanmu ne azzaluman. E mana! Don me ba zan ce haka ba???
Mune fa muka zabi wannan gwamnati,
kuma muna jin cewa tamu ce. Mun sa
mata suna “Gwamnatin mutane, wadda
mutane suka yi, domin mutane.” Kuma
muna jin mune mutanen. Da mu da gwamnatin duk abu daya ne. A wannan
hali ta yaya za mu iya cewa shugabannin
ne kurum azzalumai, amma mu ba
ruwanmu? Da mu da shugabannin -
shugabannin Kananan Hukumomi,
Da
Gwamnoni da Shugaban kasa duk cikar mu azzalumai ne, kuma duk cikarmu masu
laifi ne! Don me hakan ba zai zamo kashin
gaskiyar al’amari ba, alhali Allah Madauki
ya tsara, kuma ya kammala, kuma ya
saukar mana Alkur’ani mai girma, amma
mu muka ki kememe, muka zaba wa
kanmu tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya?
Tsarin mulki, wanda mutum hamsikanmu tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya? Tsarin mulki, wanda mutum hamsin ba
daya (49) suka tsara mana, kuma
wakilanmu wadanda muka zaba suka je
suka zartar mana? Alhali Allah Ya shirya
mana Musulunci (Islam) ya zama hanyar
rayuwarmu, amma mu muka ce a’a mu dimakradiyya muke so. Alhali Allah Madaukaki ya zarta da dokar
cewa shari’arsa za mu yi amfani da ita,!
amma muka watsar, muna aiki da dokoki
na Turawan Ingilishi! Alhali Allah
Madaukaki Ya hore mu da mu nemi gidan
lahira, amma muna jin mun gamsu da rayuwar wannan duniya kamar nan ne
matabbata. Bilhasali ma don me hakan ba
zai zama kashin gaskiya ba, alhali Allah
Madaukaki Ya hukunta cewa shi ne kawai
za a bautawa,
amma mu a maimakon
haka kasa muke bautawa. Ya ’yan uwa Musulmi! Mai yiwuwa ne abin
da nake fadi ya yi maku wuyar ganewa,
amma wallahi gaskiya nake fadi! Mai
yiwuwa ku ga kun kasa yarda, amma a
gaskiya a halin yanzu muna zaune a cikin
kafirci ne. Musulunci kam babu shi a wannan kasa! Musulunci a wannan wuri
sifiri ne, a gaskiya ma bai kai sifiri ba a
nan. E mana.
Sai dai fa muna da guggubin
Musulunci wanda ke cakude da al’adun
kakanninmu da kuma tsarin Jahiliyya,
wanda Turawan mukin- mallaka suka
kawo. Guggubin kuwa ko an tara ba zai
zama daidai da komai ba. Misalin Musulunci a wannan kasa kamar
jirgin sama ne da ya fado ya kone kurmus.
Guggubinsa da suka ragu ba za su yi
daidai da jirgi guda ba. Ko kuma ana iya
tara guggubin waje guda jirgin ya tashi?
To haka, Musulunci yake a wannan kasa. A zamanin da, an taba kafa Musulunci a
wannan kasa. Kungiyar masu jihadi a
karkashin Shehu Usman Danfodiyo karkashin Shehu Usman Danfodiyo suka
kafa shi. Daga baya sai miyagun sarakuna
suka fara kaucewa;
daga karshe Turawan
mulkin-mallaka (wadanda suke tsantsar makiya Allah ne) suka zo suka rushe
Musuluncin baki daya. Na’am. Turawa sun rushe Musulunci a
wannan kasa suka musanya shi da
al’adun gargajiyarsu, al’ada ta Jahiliyyah.
Kuma suka tabbatar cewa sun raini ’yan
kanzaginsu daga cikin mutanenmu, daga
baya suka mika rikon wannan tsari na kafirci da suka kawo a hannun ’yan
kanzagin da suka raina suka yaye. A
yanzu mu ’ya’ya da jikokin rainon Turawa
ne, ga shi a kullu yaumin muna tafiyar da
wannan nizami na kafirci, muna rayar da
shi. Hakika muna raye ne a cikin jahiliyyah ta
zamani. Muna tafiyar da ita muna tunkuda
ta gaba. Kun ga ashe matsayinmu ya fi
muni a kan matsayin Musulmi wadanda
suka ga zalunci amma suka kyale,
suka ki
motsi suka yi gum da bakinsu. Matsayinmu a yanzu shi ne na Musulmin
da suka yarda su zauna a cikin tsari na
kafirci. To, me kuke tsammani zai zama
makomarmu? Menene zai zama
hanzarinmu ga Allah Madaukaki a ranar
hisabi? A bisa abubuwan nan da na ambata, ina
yin shela a gabanku, kuma Allah
(Subhanahu wa Ta’ala) shi ne shaidata
cewa: "Ni dai na kangare wa Tsarin mulkin
Nijeriya, da tsarin dokokinta da
shugabanninta! Ban amince da ko daya
daga wadannan ba!! A maimakon haka na
dada tabbatar da imanina ga littafin Allah,
da shari’arsa da kuma shugabancin Manzon Allah (Tsira da Amincin a gare
shi)!!!" Ba zan zauna ba sai na yi maku bushara. Akwai wani hadisin Manzon Allah (Tsira
da Aminci a gare shi)
a inda yake cewa:- “A farkon kowane karni Allah zai ta da
wani wani da zai jaddada wa wannan
al’umma addininta.” Kuma alhamdu lillahi kwanan nan muka
shiga sabon karni, wato karni na 15.
Saboda haka ne ma muka zabi taken
wannan taro ya zama a kan karni na 15.
Wannan taro shi ne irin sa na 25 da
wannan kungiya ta yi. A cikinsu biyu ne kawai aka yi a wannan sabon karni. Taken wannan taro na baya shi ne wannan kungiya ta yi. A cikinsu biyu ne kawai aka yi a wannan sabon karni. Taken wannan taro na baya shi ne Imani,
wato makamin da muke bukata don rusa
wancan kafirci. Kuma fatanmu shi ne mu
ga bayyanar wannan Mujaddadi wanda
Manzon Allah ya gaya mana cewa Allah
Ya yi alkawari. Wassalamu alaikum wa RahmatullaYa yi alkawari. Wassalamu alaikum wa Rahmatullahi
Ta'ala wa Barakatuh.
_____________________
An samo ta daga Hannun Marigayi Alhaji
Hamid 'Dan Lami Allah Ya jikan shi.

Tags:
Jawaban Sheikh Zakzaky