WANNAN RASHIN IMANI HAR INA???

WANNAN RASHIN IMANI HAR INA?

An Tone Wata Gawa Tare Da Yanke Wasu Daga Sassan-Jikinta A Garin Zabin-Kudan Jihar Kaduna A Nigeria!

Daga Wakilinmu
- Abbakar Ibraheem Kudan)
Da safiyar Jiya Talata ne 25/06/2019, aka tsinci wata gawar wata baiwar Allah da aka bizne a Ranar Litini, a cikin wata rijiya ta bayan garin, bayan yanke wasu daga cikin sassan jikin gawar.



Shaidar gani da ido ya tabbatarwa da wakilin mu cewa; an tsinci gawar ne a lokacin da wani bawan Allah ya sanya guga a cikin rijiyar domin ɗebo ruwa, inda yaji alamun kasancewar mutum a cikin rijiyar, take ya zarce kofar gidan sarkin garin domin shaida masa abinda ya ganewa idanunsa.


Wata majiyar ta shaida mana cewa; ba gawa daya ce aka tsinta a yau dinba, an gano cewa an tone harda wani yaro mai kananun shaikaru da aka bizne a Ranar Litinin din, inda shima an yanki wasu daga cikin sassan jikin nasa.


Wannan dai ba shine karo na farko da irin wannan ya taba faruwa a garin na Zabin-Kudan ba. Irin hakan ya taba faruwa inda aka tsinci gawar wani bawan Allah an yanke sassan jikin sa, kimanin watanni uku da suka gabata.


Zuwa yanzu al'amarin na hannun jami'an 'yan sanda, inda suke bincike akan afkuwar wannan al'amari. Har zuwa yanzu da muke hada muku wannan rahoto, bamu samu nasarar samar muku da hotuna dangane da al'amarin ba. Allah Ya kyauta!


Daga Wakilinmu
- Abbakar Ibraheem Kudan)
Tue, Jun 25.
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post