*WANNAN CE HANYAR SAMUN 'YANCIN SAYYID ZAKZAKY (H) DA NASARAR 'YANTA QASARNAN ZUWA GA TSARIN MUSULUNCI*
Daga Wakilinmu
(Muhammad Aliyu Daud (Dansudan) Azare)070-32803940*
(Muhammad Aliyu Daud (Dansudan) Azare)070-32803940*
Sama da shekara uku, a kullum tunaninmu shine ya za a yi Sayyid Zakzaky Abba ya samu 'yancinsa, na wannan haramcacciyar tsarewar da wannan azzalumar Gwamnatin Buhari (L) take yi masa,
bayan harin da Sojoji suka kai masa bisa Umarnin Shugaban Qasa Buhari(L) da nufin kashe shi, wanda suka kashe masa 'Ya 'yansa Uku Maza, bayan ukun farko da Gwamnatin Jonathan (L) ta kashe masa.
bayan harin da Sojoji suka kai masa bisa Umarnin Shugaban Qasa Buhari(L) da nufin kashe shi, wanda suka kashe masa 'Ya 'yansa Uku Maza, bayan ukun farko da Gwamnatin Jonathan (L) ta kashe masa.
A wannan harin bisa Umarnin Buhari(L) ta kashe masa mabiya sama da mutane dubu, Maza da Mata, wanda ya hada Samari (matasa kenan) da Manya da Tsofaffi (Dattawa kenan) da kuma Yara Qanana harda Jarirai.
Wata babbar kotu a Abuja bayan Shari'a ta ce Gwamnati ta sake shi, shida uwar gidansa Ummul Shuhadah Maluma Zeenatuddeen Ibrahim, ta kuma basu diyya na Milliyon Ishirin da Biyar-Biyar kowanne, ta kuma gina musu gida a duk inda suke so a fadin qasarnan, bisa tsaresu da suka yi ba bisa Qa'ida ba, amman Gwamnatin Buhari (L) ta yi burus da wannan umarni na kotu, tana cigaba da tsare Sayyid Zakzaky Abbah(H).
Duk tunaninmu mu 'yan'uwa yanzu kamar yadda na fadi a sama shine ya za a yi Sayyid Zakzaky (H) ya samu 'yancinsa!?
Ga hanyarnan wacce ba iya nasar samun 'yancin Sayyid za ta samar ba, harda nasarar hadafin qiran Sayyid din.
Wannan hanya itace kamar haka :-
1) 'Yan'uwa mutuna da miyasa azzaluman da suka zalinci Sayyida Zahra(S.A), suka kwace mata gonarta ta *FADAK*!?.
Wanda ya kwace mata gonar cewa ya yi "In muka bar musu gonar toh, suna da qarfin tattalin arziqi, za su temakawa talakawa sosai, ta 'yanda su kuma za su bisu baza su sauraremu ba" kunji yanda ya nuna barin Gonar *FADAK* ga Sayyida barazana ne ga mulkinsu, sabida yanda Sayyida za ta rinqa temakawa mabuqata da gajiyayyu, sai ya zama cikin sauqi talakawa za su bi gaskiya su kuma rabauta, zai zamana bore da tawaye ya tabbata ga azzalumai. Sai ya zama anbi Allah da Manzonsa wanda shine basa so.
Darasin da nakeson fitarwa anan shine 'mu 'yan'uwa mu riqi kyautatawa mutane sosai da sosai, zai temaka matuqa wajen fitowar Sayyid da kuma nasar qiran da yake yi, zai kai azzalumai qasa, asirinsu zai tonu ya fito fili sosai kowa ya gane su.
Mu tuna da haka Manzon Allah (S.W.W.) ya yi nasara.
2) Mu riqi muzahara a Abuja da kuma ta bai daya a ko'ina a qasarnan. Sabida, da a mintsineka a waje daya, da a mintsineka a wajaje da yawa a jikinka wanne ya fi za fi!? Wanda aka mintsineka a wajaje da yawa ai ya fi za fi. Toh haka yake da yin Muzahara a ko'ina a qasarnan ba a Abuja kawai ba,
gwamnati ta fi jin zafin yi a ko'ina ba a iya Abuja ba. Kanajin cewa da iya Abuja kawai muke da sauran Al'ummah baza su san, irin zaluncin da aka yi mana ba, da gwamnati za ta samu damar canza musu tunani.

Tabbas yin muzahara a Abuja ta fi amfani, amman kada kace na sauran garuruwa bata da amfani, Wannan zagon qasa ne ga fafutikar samun 'yancin Jagora da kuma nasarar qiran da yake yi.
Mu tuna mana Sayyida Zainab (s.a) Shin iya Dimashqa ta tsaya wajen isar da mazalumiyar da aka yi musu a Karbala!
Da badan isarwar da Sayyida Zainab tayi-tayi a ko'ina ba da saqon waki'ar Karbala bata riskemu ba. Da ace neman haqqinsu a waje daya kawai ta yi da kuwa an manta da Karbala. Amman muduba hasalima sabida haka ba a Madina tai wafati ba, a Siriya (Syria) ta yi Wafati.
*DON HAKA MUZAHARA A KO'INA ITA CE NASARAMU, AMMAN TA ABUJA TA FI* Wannan haka yake.
3) Na uku shine muyi koyi da Manzon Allah wajen sakawa, wanda ya yi mana mummuna da alkhairi da haka Manzon Allah ya yi nasara,
mudubi misali daga gareshi An ruwaito mana cewa " A kwai wani kafiri da kullum gidan Manzon Allah nanne bolarsa, nan yake zuba shararsa in ya yi, sai Manzon Allah ya debe, kullum haka, Manzon Allah bai taba yi masa magana ba, watarana sai aka kwana biyu bai zuba ba, shine Manzon Allah ya tambayi ina ya ke, shi ne aka ce ai bashi da lafiya ne, Manzon Allah ya kai masa ziyara ya gaishe shi, wannan dalili yasa a take ya musulunta.

Da kyautatawa maqiyi Manzon Allah ya yi nasara bada yaqi ba.
Muma nasarar 'yancin Sayyid Abba yana ga haka da kuma nasarar qiran da yake yi.
4) Na hudu Shine son junanmu da yin aiki a tare da afuwa ga juna. Manzon Allah ya ce "Baza ku yi Imani ba har sai kunso junanku......" A qur'ani Allah yace:- "lnnamal mu'uminina Ikwatun, fa aslihu baina akwaikum wattakullaha La'allakum turhamun" Fassara "Su muminai 'yan'uwan junane, ku daidaita tsakanin 'yan'uwanku,
kuji tsoron Allah sai ya yi muku rahama" A wata Aya kuma Allah ya ce: "Muhammadun Rasulullah Wallazina Ma'ahu ashudda'u alal kuffari Ruhama'u Bainahum....." Fassara "Muhammad Manzon Allah ne, wa 'yanda suke tare dashi suna da tsanani ga kafurai, suna da Rahama a tsakaninsu"

Tabbas hadin kanmu shine nasarar samun 'yancin Sayyid da kuma qiran da yake akai mu lura da wannan sosai.
Daga karshe 'yan'uwa mu Lura kada mu bawa azzalumai damar tarwatsamu da qiran da Malam yake ga Al'ummah. Sayyid ya daura harqannan bisa tsari kada mu bata tsarin da ya yi da kansa tun kafin waki'a, Wannan tsarin azzalumai suke tsoro don shine nasarar Qiran da Malam yake. Duk wani mai cewa a sabawa tsari toh yana yiwa Jahiliyya aiki ne! Imam Ali (a.s) yana cewa "Kuji tsoron Allah ku tsara Al'amuranku".
Daga Wakilinmu
(Muhammad Aliyu Daud (Dansudan) Azare)070-32803940*
Daga Wakilinmu
(Muhammad Aliyu Daud (Dansudan) Azare)070-32803940*
*FREE ZAKZAKY(H) WA UMMUNAH ZEENATUDDEEN*
Tags:
#FREE_ZAKZAKY