-Cewar Sheikh Adamu Tsoho Jos.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates tare da -Idishia Jos.
Musamman ku da kuka zo wannan ziyara ku 'yan Media ne, yana da matukan muhimmanci ku iya fahimtar rawan da zaku taka a tafiya na gwagwarmayan Musulunci a wannan marhala da muke ciki na jarrabawa kuma marhala da muke ciki na rashin jagora a cikin mu, yana da muhimmanci ku fahimci menene zakuyi a lokacin da makiya suke yakan mu ta inda muka sani da inda ma bamu sani ba, wani gudumawa zaku bayar! Idan muka duba a wannan lokacin Media ta zamo hanya mai girma mai muhimmanci wajen kawo sauyi a cikin al'umma.
An kai ga a wannan zamani su kansu turawa da suke cewa Gwamanti ta rabu kashi Uku akwai abinda ake kira Executive, Judiciary, Legislative wato akwai bangaren shugaban kasa mai iko wanda yake zartar da abu, kuma akwai bangaren su 'yan majalisi wanda sune suke kafa dokoki ko fitar da ka'idodi, sannan kuma akwai bangaren masu zartarwa. To a wannan zamani da muke ciki yanzu sun gano cewa Media shima wani bangare ne na Gwamnati, saboda duka waccan bangarorin ba zasu iya yin nasara ba in ba Media, bilhasani ma da Media za'a iya canza al'umma acan za gwamanati a datar da mutane daga wata fikira akai zuwa fikira mai kyau.
Don haka a matsayin ku na 'yan Media kuma 'ya'yan Harka Islamiyya dole ku fahimci girman aikin da ke gabanku da kuma abinda ya kamata kuyi, a cikin aiki na dan Media ko'ina a ka'ida ta duniya ka'ida ta aikin Media, shi dan media baya zamowa dan wani bangare shi dan bangaren gaskiya ne, shi yana tsayawa a bangaren gaskiya ne. Gaskiya ma wanda zai taimakawa al'umma ya cigabatantar da al'umma ya wayarwa al'umma kai da fadakarwa ita al'umma a daura su akan tafarki madaidaici, yana daga cikin ethics na 'Journalism' da sauransu haka.
Akwai wahaloli da sauransu a aikin media 'Genaral' wanda ma ake biyansu kenan, amma mu a harka duk wanda kaga yana bada gudumawa bawai ana biyansa bane kowa shi ya kawo Kansa, kuma yana yin abin yake yi ne domin ya sauke wajibin da ya dauri a kansa, irin baiwan da Allah ya maka to ta nan ne ake so ka bada naka gudumawa. Idan kai Allah ya baka karfi to a harka musulunci inda ake bukatan karfi sai a ganka a wurin, idan Allah ya baka dukiya ne wajen bada gudumawa na dukiya harka tana bukata sai a ganka a gaba-gaba ko kuma ilimi duka dai kowanne mu Allah zai tambayeka akan irin abin da Allah yama na baiwa.
Ba muna yin wannan ne ko dan abin duniya ko dan mu samu wani Abu ba a'a neman uziri ne gaban Allah, kamar yadda su Malam (H) suke nuna mana an taimaka maka ko ba'a taimaka ba kai zaka tsayu tsakanin ka da Allah ka bayar da naka gudumawa da fatan Allah ya kar ba yasa a cikin kyawawan mizanin ka in kuma ka samu haka to ka rabauta duniya ka da lahira. Kaga aikin Media ba zaka saurara ba kamar yadda su yan Media na waje wanda suke bangarori daban-daban ana basu albashi kai ne ma zaka nemi kayan aikin ka, kai ne zaka bubbuga ka sayi Data kaine zaka bubbuga kaje nan kaje nan ka samo bayanai ko ka dauko abinda zaka dauko wanda zai cigabantar da ita harka.
Don haka kada rashin ainihin gudumawa daga 'yan uwa ya sanya ka yi rauni, ka dauka shine baiwan da Allah ya maka kuma ta nan zaka iya bada gudumawanka wa Harka musulunci. Kuma ya zama kana yi tare da ikilasi kayi don Allah ba don wani ba, kana fatan Allah ya karba yasanya a cikin mizanin kyawawan ayyukan ka wannan in an samu haka shine kayi babban nasara. Don haka a halinda muke ciki 'yan Media dole su san menene zasu rubuta menene zasuyi rubuta su yada menene ba zasu yada ba. Kamar yadda mukace Media ya dauru akan gaskiya duk Media na duniya ka'idansu dole ya zamo ka tsayu akan gaskiya ka samo labari na gaskiya ka isarwa mutane.
Insha Allah zamu cigaba a kashi na biyu anan ne zamuji abinda ya wajabata akan mu kuma me ya kamata ace munyi a matsayin mu na 'yan Media Harka Islamiyya don Isar da sakon Harka ga Mutane baki daya. Wannan wani bangare ne na jawabin Sheikh Adamu Tsoho Jos da yayi a lokacin da aka kai mai ziyarar Sallah na 'yan Media Cikin garin Jos.
#FreeZakzaky

Sheikh Adamu Tsoho Jos tare da wasu wakilan Media Mata bayan an kammala Jawabi |

![]() |
Sheikh Adamu Tsoho Jos a lokacin da yake addu'a bayan kammala jawabi ga 'yan Media. |
#FreeZakzaky
Tags:
Tunatarwa