{TAWAYE GA HIJAB LAIFIN IYAYE NE A LOKUTAN SHAGULGULAN SALLAH}

TAWAYE GA HIJAB LAIFIN IYAYE NE A LOKUTAN SHAGULGULAN SALLAH!!!
Daga Wakiliyarmu___*{Fatima Xahrah Shi'ite}*

Zakaji Iyaye Musanman Mata suna fadin cewa Kowa fa Gyalen nan yake sawa ai ita kwalliyar Sallah in aka sa Hijab batayin kyau:
Kuma abin Mamakin sai kaga Mahaifi Namiji yana bakin Qoqarinsa wajen ganin 'Ya'yansa Mata sun fita da shiga ta kamala amma a mafi yawancin lokuta sai kaji iyaye mata na fadin yanxu fa dole sai da Kwalliya Samarin Zasu gani suce suna so Zamani ya Chanja, idan iyaye Maza suka takura sai 'Yarsu tasa Hijab sai kaji iyayen Mata suna fadama 'Ya'yan nasu cewa Su dauki Gyalen ki boye ki tafi dashi in kinje Hanya sai ki cire Hijab din kisa Gyalen wannan ya faru a gabana,

Ita Mahaifiyar tana ganin cewa idan 'Yarta tayi kwalliya tasa Gyale tana rangwada a titi shine zaisa ta samu Miji Guy Mai Kudi
Duk Budurwar da Mahaifiyarta take sanyata a irin wannan Hanyar Tun anan zaki tabbatarma kanki Bakiyi Dacen Uwa Tagari ba, domin duk Uwa tagari bazata so 'Yarta tayi Shigar da bata dace ba
Ina Matukar Mamaki idan naji ana cewa sai da kwalliya da Matsattun kaya da Karamin Gyale ake Samun Mijin Aure ,:



A yayin da kikayi shigar da bata dace ba kika fita duk wanda kika ji ya yaba Kwalliyarki to dama shima dai sai a Hankali
Indai Mace tanaso ta sami Miji nagari mai kamala wanda Zaisan daraja da kimarta bayan sunyi Aure To Taci gaba da shigar Mutunci wadda Addini yazo mana dashi
Tabbas zai rinka Mutuntata tunda dama da Mutuncinta ya ganta.
Sisters Almajiran Sayyid (H) Ansanmu da Sanya Hijab da kuma kare Mutuncin Hijab din A ko'ina fatan zamu cigaba da kare mutuncinmu da darajarmu.!

Shawara ce!!!
Allah yasa mudace.
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post