*TARIHIN IMAM KHUMAINI (KS) FITOWA TA BIYU*

*TARIHIN IMAM KHUMAINI (KS)*

Fitowa ta biyu (!!)
Daga Wakiliyarmu
(Sakina Ahmad Kazaure)

TAKAITACCEN TARIHIN GARIN KHUMAINI,

Khumaini wani birni ne dake sashin kudu maso gabas a cikin tsakiyar lardin kasar Iran. Ya kasance tsohon birni dake kewaye da kauyuka guda 90 kuma za'a iya kallon sa a matsayin birnin da ya kasance a cikin tarihi Wanda yayi kusan shekaru 1,511.


 Kuma an bayyana cewa *HUMA* yar *BAHMAN KIYANI* ce ta gina shi. Sunan wannan birni ba asali shine *KHOMAYHAN* Wanda yake nufin *KHO (kyakkyawa)* *MAYHAN kuma wuri*. Anan in an hade ma'anarsu wuri daya zasu bada ma'anar wuri mai kyau. Garin khumaini da sauran kauyukan dake kewaye dashi ana kiran su da suna kamare'i. Anan ana nufin duk mutumin da ake kiransa ko iyalin sa ko dangin sa da suna kamare'i hakan na nufin shi da kakanninsa an haife sune a wannan kauyukan dake kewaye dasu.


Gidajen dake khumaini kamar gidajen dake tsakiyar garin Iran ne domin an gina su da busassun duwatsu na wuta an kuma shafe su da tabo sannan kuma an rufe su da manyan katakwaye masu karfi kuma gaban ginin an masa shafe da tabo mai kyau Wanda aka hada shi da ciyawa sannan kuma akwai wasu gidaje kadan a kowane bangare da aka kewaye gaban su da manyan duwatsu wasu kuma anyi masu rufi mai karfi domin kariya daga kankara da kuma ruwan sama.



gaba daya yanayin garin khumaini yayi kama da gulpaygan da kuma khansar wato wasu garuruwa biyu da suke makwabtaka da garin khumaini. Mafi yawan sassan birnin cike suke da ruwa  sannan shuke-shuken dake wurin masu yaduwa ne ga kuma koramu masu yawa da kuma kayan lambu masu kayatarwa.



Koramun da suke garin khumaini sun karawa garin yanayi mai kyau da kuma jan hankali. Saboda hasken tsaunin alwand wani dutse mai gasken gaske Wanda za'aiya ganinsa daga zango mai nisa. Haka kuma garin khumaini bai kasance birni mafi shahara ba a Iran kuma bai kasance birni mafi kyau ba, kuma bashi da takamaiman yanayi kamar sauran birane. Amma Abu mafi muhimmanci game da birnin shine samun wani mutum Wanda ya bayyana a kusan farkon karni a lokacin da manyan mutane suka zama yan siyasa shi kuma ya kasance mai riko da addinin musulunci.


Kuma sunan shi wannan mutumin an ciroshi ne daga wannan gari. Bayyanar wannan mutum yayi tasiri a ilahirin taswirar duniya, a inda yaci gaba da kasance wa mai muhimmanci a cikin tarihin duniya.


*NASABAR IMAM KHUMAINI*


Nasabar imam khumaini ta tuke ne zuwa ga manzon Allah (s). Asalin kakanninsa daga Makkah suke suka taso suka dawo farisa.don haka imam khumaini balarabe ne na asali amma shi an haife shine a farisa (Iran) a farkon karni na 20.


   Nasabar imam khumaini tana tukewa ne ga imam musa bn jafar alkhazim imami na 7 daga cikin jerin a'immah   (a.s) imam musa ya kasance yana zaune a khumaini, sai khalifa na abbasiyyawa al-mahdi ya shirya wani makirci tare da wasu mutane aka kira imam musa (a.s) domin ganawa da shi. Daga nan aka kamashi aka kulle shi a cikin kurkuku. Kabarinsa yananan har yanzu a hedikwatar iraki a kazimiyya bagadaza.


   Bayan shahadar sa wasu daga cikin ya'yan sa sunyi hijira zuwa neshabur, Wanda take a cikin kasar Iran a halin yanzu. Anan suka zauna tsawon lokaci kafin kuma daga baya suyi hijira zuwa khashmir, ana kiransu 'ya'yan musawi.
Bayan sun isa khashmir sun bada gudunmawa yadda ya kamata wajen bunkasa addinin musulunci Anan sukayi da hayayyafa har aka haifi mir Hamid husayn al-musawi. Shine kakan imam khumaini na uku kuma tsakanin sa da imam khumaini shekara 250. Kuma shi ya rubuta littafin nan mai suna abakatul anwar a India a inda Allah yayi masa rasuwa a can.



Mir Hamid husayn yana da ya'ya guda biyu duk maza wato Hamid da kuma din Ali shah. Sunyi shahada a khashmir. Har yau kabarinsu yananan a khashmir.
Din Ali shah yana da da namiji mai suna sayyid Ahmad. Bayan shahadar mahaifinsa sai yayi hijira zuwa iraki don Karin neman ilimi a garin najaf a wajen ayatullah sayyid Mirza shirazi. Kafin sayyid Ahmad yazo iraki sai da ya ketare India shiyasa ake kiran sa Ahmad al-hindi. Sai dai zaman sa a iraki na kankanin lokaci ne.!


*BAYYANAR SAYYID AHMAD*

Daya daga cikin garuruwan khumaini ana kiran sa farfahan, kamar wani bangare ne  Wanda ya hade da wani gari mai suna farsakh na khumaini. Mutanen wannan gari karkashin jagorancin Yusuf khan sun tafi najaf wajen ayatullah sayyid Mirza shirazi don ya taimaka masu ya basu malami Wanda zai taimakesu bunkasa addinin musulunci a garin khumaini.




   Daga cikin malaman musulunci sai ya zabi allamah sayyid Ahmad Hindi Wanda yake da wani tambari a goshinsa na soyayya, kuma baya tsoron yin hijira zuwa kowace kasa domin kakanninsa ma haka suka kasance wajen yada addinin musulunci. Sayyid Ahmad yayi masu jagorancin komawa khumaini. Da suka iso mutanen wannan gari sunyi farin ciki yadda ya kamata sannan suka zabeshi ya zama shine babban malami kuma mai hukunci a tsakanin su.






Muhammad husayn yana daya daga cikin fitattun kauyen farfahan Amman daukakarsa ta kaishi Ku sa da dangin da suke da ilimi ba masu mulki ba. Yana da yaya biyu daya namiji ana kiran sa Yusuf Wanda mabiyi ne na kusa da sayyid Ahmad a cikin buruni, dayar kuma mace ce Wanda ake kira sukhainah Wanda ta zama matar sayyid Ahmad. A cikin wannan gida ta haifi 'ya'ya hudu uku mata na hudun kuma namiji ne. A ranar alhamis alokacin da rana ta dago kololuwar sama sai aka haife shi sun samo suna daga cikin sunayen manzon Allah (s) sun saka masa wato mustapha.
Sayyid Ahmad yana da.wasu mata guda biyu akwai shirin wadda take 'ya ce ga abid gulpaygani, sai kuma bibijan wadda take 'ya ce ga karbala'i sadr Ali khumaini daya daga cikin su itace ta haifi dansa na farko mai suna murtada. Yayi karatu kuma ya zama malami amma kafin ya samu damar yin aure Allah yayi masa rasuwa alokacin da yake cikin kuruciyar sa, shekara daya bayan mutuwar mahaifinsa. Saboda haka mustapha dansa guda daya shine ya rayu lokaci mai tsawo shi da yan uwan sa mata.

*SAYYID MUSTAPHA DAN SAYYID AHMAD*

A gabansa mutane suna kiran sa aka, idan kuma baya nan suna kiran sa aka sayyid hindi. Idan za'a fassara wannan zuwa larabci za'a samu kalmomin "sayyid" guda biyu wato daya ta aka Wanda ma'anar ta shine sayyid dayan kuma shine Wanda duk wani jikan manzon Allah (s) ana kiran sa sayyid kafin sunan saboda haka aka mustapha sayyid ne.


   A cikin gida yana sa farar hula a kansa amma a waje yana sa bakin rawani da duk wani sayyid yake sawa wata alama ce ta bakin cikin mai dorewa saboda kashe kakansu imam Hussain (a.s).


Sannan kuma duk wani sayyid Wanda rushen sa yake zuwa ga imam musa al-khazim (a.s) imami na 7 cikin imaman Shi'a wannan mutum ana kiran sa musawi.
 A bangaren abin da ya shafi ilimin karatun addinin musulunci Wanda yake mataki na farko dai-dai yake da B.A (wato digiri na 1) a zamanin yanzu. Sannan kuma mataki na gaba wani lokaci daidai yake da M.A (wato digiri na2) a zamanin yanzu irin wannan sun can can ci suyi wa'azi na addini. Idan yasa labbadeh wato Riga irin ta malamai sannan kuma yasa abaa( wato abaya) a kafadin sa, da kuma rawani a kasansa awani biki na musamman za'a iya kiran sa hujjatul Islam.



Aka sayyid mustapha musawi da farko ya karanci wasu yan litattafai a khumaini a wajen aka mirzi Ahmad khansari Dan mullah Husain khansari malamin ya bude masa gidansa da kuma kofofi, farko ya fahimci cewa wannan yaro maraya ne don haka malaminsa yakan ziyarce shi a wasu lokuta shi da matar sa da kuma dansa. Sukan zauna a barandar gidan domin daukar karatu a duk lokacin da malamin sa yake masa karatu sai wata 'yar sa mai suna hajiya agha sai ta fito tana kewaya baban ta idan ta gaji sai ta zauna akan cinyar sa. Sannan kuma yanayin nazari da kuma bitar abin da ya koya.




   Alokacin da aka sayyid mustapha ya tafi Isfahan a wannan lokacin cibiyar ta Samar da mashahuran malamai. Sannan yayi karatu afannoni da daman gaske daga ya dukufa a wajen Neman ilimi har yazama hujjatul islam, daga nan ya tafi najaf domin ya karanci ilimin fikihu a wajen marigayi Mirza shirazi, Wanda shine shugaban yan Shi'a a lokacin.




   Alokacin da yabar cibiyar ilimin tauhidi wato hauzah sai tunanin aure ya fara zo masa a cikin ransa San nan kuma yaga ba wadda ta dace da shi sai hajiya agha wadda ya dauki shekaru da yawa bai gani ba. Duk da cewa yanzu yasan ta girma yayin da ya aika sakon sa na nema sai ya samu kyakkyawar amsa daga baban ta da kuma ita kanta. Sai ya koma khumaini a inda ya Isar da bayani da kuma sauran tsare-tsaren biki. Bikin ya samu kyakkyawar karbuwa inda kusan rabin mutanen alkaryoyin guda biyu na khumaini da kuma khansar duk sun samu halarta. Mahaifin amarya ya kasance daga khansar yake,don haka mafi yawan mutanen khansar an gayyace su, domin su bayyana tasu murnar. Aka mustapha ya samu kwarin gwiwar shawartar matar sa domin ta canja sunan ta izuwa hajar kuma ta so wannan suna, ta kuma can za shi har abada  bayan sati guda sai yayi bankwana da dangin sa ya koma Isfahan shi da matar sa don zama a can.
 


   Sannan duk Wanda ya fahimci fikihu fahimta ta hakika bashi bukatar kwaikwayon wani irin wadannan bayin Allah ana kiran su mujtahidai sai kuma a basu mukamin ayatullah Wanda a zamanin yanzu dai-dai yake da P.h.d( wato digiri na uku). Aka sayyid mustapha malami ne Wanda ake kiran sa ayatulkah wato ya kasance mai fikira har ya kasance zababbu na khumaini suna kiran sa fakhrul mujtahid. Mutane sunyi jira na tsawon shekara 27 domin ya dawo garin su ya maye gurbin mahaifinsa. Yayin da gayyata ta zama gagaruma kuma aka kara mai mai tata sai yaji bazai ki zuwa ba saboda haka sai ya dawo kuma ya zauna a gidan da aka haife shi tsawon shekara 8 kuma akwai alamun ya maye gurbin shugabancin makarantar addini a cikin khumaini mutane sun yarda dashi kuma yaso mutanen sa da zuciya daya.



Aka mustapha yana da 'ya'ya guda biyar kuma an haife su ne a wannan daki kuma akwai tabbacin cewa na farko shine mawlud aka, Wanda aka Haifa a najaf.sannan kuma a lokacin da shi aka mustapha yake karatu a Isfahan ya dawo da matar sa hajar khanun domin ta haihu a cikin khumaini domin ta samu kulawar mutanen ta. Yar ta ta biyu mai suna Fatima Wanda ita ma an haife ta ne a wannan daki sai kuma aka murtada Wanda alokacin yake fanfaran hakori da kaninsa nuraddin suma an haife sune a wannan daki. Karamin Dan aka mustapha shine aka zaden khanum Wanda alokacin ake shayar dashi shima a wannan daki aka haife shi.



Bayan wani lokaci mai tsawo aka mustapha da hajar sunyi ta jiran wata haihuwar ta faru a wannan daki kuma dukkanin su suna jira sannan kuma a wannan lokaci a cikin biruni mutane sunata zuwa domin taya aka mustapha murnar bikin kausar kamar yadda dukkan gari ake ta bikin zagayowar haihuwar yar manzon Allah (s).

 

Zamansa haka kawai sai ya janyo masa rashin hutu kaguwa da murna suna ta daduwa saboda haka sai murna da zumudi suka dada rashin hutun sa. Babban dalilin da yasa zuciyarsa take bugawa watakila saboda a wannan lokaci ziyarar bikin sa ta hadu da bikin haihuwar yar manzon Allah (s) sayyida zahra (s.a) sannan kuma a dai-dai wannan lokaci matar sa hajar tana gab da haihuwa don haka aka mustapha yayi alkhawarin cewa idan jaririyar mace ce sunan ta zai kasance zahra kasancewar yar sa ta biyu tana da suna Fatima.

Muhadu a kashi na (!!!)
*(sakina Ahmad kazaure)*


Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post