*(TARIHIN IMAM KHUMAIN (K.S KASHI NA DAYA {!}
GABATARWA
*MA'ASUMA NIGERIA NEWS UPDATE*
Daga Wakiliyarmu
{Sakina Ahmad Kazaure}
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Wanda ya aiko manzonsa domin ya kasance rahama ga talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga wannan manzo da iyalan gidansa tsarkaka wadanda ya ambace su tare da littafinsa a matsayin halifofi a bayansa.
Yazo acikin hadisi daga aba huraira yace: "manzon Allah (s)ya karanta wannan ayar" idan kuka juya baya zai musanya Ku da wadasu mutane ba kuba." Yace: manzon Allah (s) ya Dora hannunsa mai albarka akan cinyar salamanul farisi yace: wannan da jama'ar sa, na rantse da Wanda raina yake hannunsa da addini (imani) zai kasance rataye ga tauraruwa surayya da mazaje daga farisa sun dauko shi" (aduba a cikin tarikh al-isbahan da tafsirin dabarani.)
Daga aba huraira yace: a yayin da aka saukar da wannan aya idan kuka juya baya... Manzon Allah (s) yace: zai iya musanya wadansu mutane wadansun Ku sa'annan bazasu kasance kwatankwacin Ku ba. Sai suka ce: ya manzon Allah su wanene wadannan? Salmanul farisi ya zaune sa'annan yace wannan da jama'arsa. Na rantse da Wanda raina ke hannunsa idan da biyayya zai ko addini zai kasance lankaye ga tauraruwa surayya da wani mutum daga farisa ya daukoshi."
Wannan hadisi ya fito a tafsir al-dabari da tafsir ibn sa'ud da durrul mansur da mustadrak na hakim daga said ibn mansur da ibn jarir da ibn manzur da ibn hatim da ibn mardawiya.
kurdabi yana cewa a cikin *umdatul kari* mafi dacewar tafsirin" wadansu mutane "shine mutanen farisa. Dalili kuwa shine addini ya bayyana a cikin su kuma da yawa daga cikin su malamai ne. Kuma wannan ya zama dalili na gaskata annabcin manzon Allah (s).
A yayinda aka saukar da ayar nan ta suratul ma'ida inda Allah madaukakin sarki ke cewa: da sannu Allah zai zo da wasu mutane yana son su kuma suna son sa...." Sai suka tambayi manzon Allah (s) Dangane dasu sai ya daki kafadar salmanu sa'annan yace da imani zai kasance lankaye da surayya da mazaje daga yayan farisa sun dauko shi.
Idan mukayi la'akari da wannan ayar zamuga cewa an ambaci siffofin wadannan mutane kamar haka:-
*1 yana son su kuma suna son sa*
*2 masu tawali'u akan muminai masu izza kan kafirai kamar dai yadda yake fadi a wata ayar "masu tsanani akan kafirai masu rahama a tsakanin su"*
*3 suna jihadi a cikin hanyar Allah*
*4 kuma basa tsoron zargin duk wani mai zargi*
*5 wannan falalar Allah ce yana bayar da ita ga Wanda ya so kuma Allah mayalwaci be mai ilimi.*
Alokacin da shugabannin kwatar yanci na yan kishin kasa ko na yan yakin sunkuru ko sari ka noke suke faman fito na fito da dauki ba dadi da azzalumai fir'aunawa kuma masu mulkin kamakarya da yan korensu sai kaji suna ta zakin baki suna cewa tilas ne ko ana haaa maza haaa mata sai an samu tsarin harkokin kasar waje irin na yan ba ruwan mu.Amman tun tafiyar batayi nisa ba sai kaga sun fada tarkon kungiyoyi yan koren manyan kasashen duniya masu dagawa.
Amma shi imam khumaini (ks) don gaskiya ake tsoron sa ya kuma nuna rashin amincewar sa ga karkata ga wata kasa a fannin siyasa,soja,da tattalin arziki. Tun farkon yunkurinsa har zuwa ranar da akayi nasarar kafa jamhuriyar musulunci. Haka ya tafi da wannan lamari ba sassauci ba ja da baya.
Cikin shekaru goma da motsi bayan nasarar juyin musulunci duniya taga irin nasarorin da kuma gagarumin sauyin da aka samu a kasar Iran. Musamman dangantakar kasar Iran da sauran kasashen duniya.saboda kar masu karatu su dauka mutuniyat muke shararawa (karya) bari my kawo maku wasu yan misali.
Soke duk wasu yarjejeniya da rubutattun alkawuran da aka kallafawa Iran ko aka yi mata shigo-shigo ba zurfi kamar yarjejeniyar da aka kulla a shekarar 1959 tsakanin ta da kasar amurka Wanda ta bawa amurka hakkin yin ruwa da tsaki da tsoma baki a cikin harkokin cikin gidan Iran. Da kuma murtsuke takardar yarjejeniyar da akayi tsakanin tarayyar sobiyet da Iran a shekarar 1921,inda akace rasha tana da ikon tsoma baki a cikin al'amuran sojan Iran.
Sannan kuma an janye huldar jakadanci a kasar amurka, isra'ila, afirka ta kudu da kasar masar. Da katse dangantakar diflomasiyya da kasashen da suke taimakon isra'ila da rufe kamfanonin da suke mu'amala da ita.
Yin Allah wadai da mamayar da kasar da kasar rasha tayi wa Afghanistan da nuna goyon baya ga kungiyoyin jihadi da na kwatar yanci a duniya kana da shiga kungiyar yan ba ruwanmu.
Imam khumaini(ks) yaci gaba da wannan gwagwarmaya hatta lokacin da ya taba kwanciya a asibiti. Inda yake cewa daga nan asibitin ina gargadi ga raunanan kasashe da suyi hankali da manyan kasashe masu dagawa. Ina kuma kiran su dasu hade kansu don su yantar da kasashen su daga danniyar amurka da sauran manyan kasashe. Zamu fuskanci wadannan shedanu da duk karfin su."
Hakana wajen harkoki da sauran kasashen musulmi, imam khumaini (ks) yafi bada karfi ga al'ummomi mai makon hukumomi.
Daga karshe ina fatan wannan rubutu ya zama jagora ga mai karatu wajen sanin irin gwagwarmayar wannan bawan Allah abin koyi.
Tare da yar karamar autar Ku
*{sakina Ahmad kazaure}*

Tags:
Muhimman zantuka