TAQAITACCEN JAWABIN WAKILIN 'YAN'UWA NA GARIN NINGI !!!
Daga Wakilinmu___
( Ado Isah Guda)
( Ado Isah Guda)
Kamar yadda aka saba a kowacce sallah ta azumi ko lahiya, bayan saukowa daga sallar Idi 'yan'uwa kan taru a Markaz don cin abinci da kuma sauraron taqaitaccen jawabi (Kass) daga bakin wakilin 'yan'uwa:,
Cikin jawabin nasa, malam Yusuf 'Dahiru Bununu ya bayyana watan Ramadan a matsayin makaranta ta samun taqawa kamar yadda Allah (T) ya ambata, !
Yace kamar yadda ake kebe Sojoji ne a ba su (training) na cire musu mutuntakar dan Adam farar hula (civilian mentality), to, shima Ramadan ya kasance wata ne da ake kebe bayin Allah don tarbiyyantar da su kyawawan dabi'u (moral attitude),

Yace, watan yana qara kusanto damu zuwa ga tsoron Allah, sannan ya koyar da mu jin qai, tausayi da kuma juriyar hanawa kanmu abubuwan da zuciyarmu ke so yayin azumin,
Malamin ya bayyana cewa duk wanda ka ga bai koyi ciyarwa (Imfaqi) ba a bayan watan azumi, to, azumin nasa bai fa'idantar da shi Komai ba,!
Ya gargademu kan cewa mu kasance masu yin haquri da junanmu, ka da ka dauki dan'uwanka a matsayin abokin gaba don ka sami 'yar matsala tsakaninka da shi.
Akwai wata magana ta sirri mai kama qwaqwalwa da ban tsoro,!
Amma kasantuwar a junanmu ('yan Shi'ah) ya kamata mu sani ba zan kawota anan gurin ba, !
Amma kasantuwar a junanmu ('yan Shi'ah) ya kamata mu sani ba zan kawota anan gurin ba, !
A qarshe ya gargade mu da cewa mu sani, duk wanda ya aikata wani aiki da zai yi sanadin rabuwar kai tsakanin 'yan'uwa, to, ya sani Yahudawa da Jahiliyya ya kewa aiki.
Daga Wakilinmu Na Yankin Bauchi Da Ningi (Ado Isah Guda)
08126385470-08137925034
Tags:
Muhimman zantuka