SUNNAR ALLAH BATA CHANZAWA

Kashi na Farko (01).

🇳🇬 Ma'asumiyah Nigeria News Update tare da : @Isma'il Abubakar Idris Katsina.

Kadan daga cikin Jawabin Sheik Ibrahin Yaqub El-zakzaky mai suna "Sunnar Allah bata Canzawa".

Wannane lokaci na farko dana fara tsayawa gaban mutane tunbayan da nafito daga Makaranta Kur-kuku afarkon Azumin Ramadan shekara ta 1998 wadda ta wuce wanda
Gwamnati ke Tuhimata akan nace " Babu wata Gwamnati saita Musulunci".

Kada kuyi tsammanin jin wani abu sabo daga bakina sai dai wanna abin wanda aka sabaji shi ne za'aji domin haryanzu yananan a marhalar Da'awa domin haryanzu bamu wuce wanna marhalarba, Marhala irin wadda Manzon Allah wadda ya kwashe Shekara (13) a Makka yana kanta ta Marhalar Tabbatar da Addini batare da mutane sun yarda da ita ba.

Wanna Marhalar Irinta Annabi Nuhu wadda ya kwashe shekara (950) yana kanta, haryabar duniya baiwuce wanna marhalarba, a wanna marhalar ya tsaya har Allah ya kawo karshen wadannan azzaluman.

Yaushe wanna Marhalar ta tabbatar da Addinin Allah zata kare, abun ba'ahannunmu yake ba yana hannun Allah ne, Munanan akan Marhalar Sunnar Allah wadda bata canzawa, da wanna Sunna ta Allah yasaba Jaraba dukkan Manzannin da ya aiko.

Allah ta'ala daya haliccemu ya doramu bisa cewa dole saiya Jarabcemu ta kowace hanya gwal-gwadon Imaninka gwal-gwadon Jarabawarka, tundaga zuwan Annabi Adam har zuwa yau wanna sunnanar ta Allah ita kadaice kwara daya (1) ba ta taba canzawa.

Daga Annabi Adam zuwa Annabi Muhammad (S.a.w.w) marhalace ta sunnar Allah, idan al'umma suka koma bin wanin Allah kamar yadda Jama'ar Annabi Nuhu suka kasance ko Jama'ar Annabi Shu'aibu ko Jama'ar Annabi Lu'ud da kuma Annabawan bani Isra'il Tundaga Annabi Musa da Yushe'u harzuwa Annabi Isa duk cikarsu Sunnar Allah sukabi basu taba canzawa ba!.

Mafi yawan Al'ummar da Annabawa ke kira zuwa ga Sunnar Allah kalilan ne ke amsa wannan kiran.
Muhadu kashi na Biyu (02).

Kuna Tare da Shafinku na : 🇳🇬Ma'asumah Nigeria News Update.

 Ku ziyarci Wep site :Www.Ma'asumahNigeriaNewsUpdate.

 Shafikan mu :Facebook, WhatsApp, Youtube, Tweeter, Shazam, Wechat.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post