Cigaban Jawabin Sheik Ibrahim Yaqub El-zakzaky mai suna "Sunnar Allah bata Canzawa", Wanda yayi a Shekara ta 1999.
Allah (t) zai tabbatar da addininsa bayan mamugunta sunyi duk abinda sukai niyyar yi alokacin da Mabiya Sunnar Allah suke 'yan kalilan bayan wasu al'umma sun koma gefe guda. 'yan baruwansu sunzama 'yan kallo.
Duk lokacin Allah ya turo wani manzonsa sai wasu al'umma sudauki matakai akan wanna manzon wasu kuma su gallazama wanna Manzon ko kuma suyi yinkurin kasheshi, in Allah yaso zai tsamarda wadanda sukayi imani da wannan manzon sai ya hallaka basuyi imani dashiba batare da yaragu ko ya karu da komi ba.
Allah shikeyin yadda yaso ba yadda kaso ba, dai-dai gwalgwadon darajar mutum wajen Allah dai-dai gwalgwadon wahalarda yakesha ga Al'ummarsa tamkar yadda Allah ya jarabci Annabi Nuhu da sauran Annabawan bani Isra'il da Annabi Muhammad a lokacin Hijirarsa daga Makka zuwa Madina a lokacin ne suka bishi har suka fasama Manzon Allah kai.
Annabawan bani isra'il Allah bai kyalesu hakannan ba saida ya turomansu manzani, tamkar yadda Allah yayima wanna Al'ummar da Annabi Muhammad (S.a.w.w) Allah bai kyalesu hakanan ba.
Babu wata hanya wadda mutum zaisamu abu cikin sauki ko minene Kudi ko Mulki ko ilmi balantana addinin kayan Allah.
Dukkan mai da'awa da bara'a yace " la'ilaha'illallah ita za'abi ba tsarin wanin Allah ba zakuga ya fandarema tsarin wanda bana Allah ba!".
Addinin Musulunci ba ra'ayin wani bane umurnine daga Allah yadda Allah yaso haka za'ayi ba yadda gwamnati keso ba.
Ada anacemana 'yan tashin hankali muna fada da gwamnati, bamason wanzar da zaman lafiya a kasa, wannan dalilin ne yasa duk lokacinda gwamnati ta afkamana sai sufake da sunason zaman lafiyar kasa ne, zamu tada hankalin kasa zamu dora kasar bisa wani tsari ba daban.
Insha Allah Sunnar Allah zata dawo Jagoranci a Kasarnan lazim ba makawa, duk mai barci ya farka, kazo ayi dakai ko kakoma gefe kayi kallon anayi.
Tags:
Jawaban Sheikh Zakzaky