SUN GUDANAR DA GASAR MAWAQA A GARIN BAUCI


AN GUDANAR DA GASAR MAWAQA A GARIN BAUCHI
.
A jiya Asabar ne qungiyar mawaqa ta cikin yan uwa  musulmi Almajiran Sayyid Zakzaky (H) suka gudanar da gasar mawaqa a garin Bauchi wanda akayi akan Imami na hudu daga cikin jerin limaman Shiriya, wato Imam Aliyu Zainul Abidin (as) a garin Bauchi.
Mallam muhammad abbare kenan tare da ba'adin wasu daga cikin mahalarta taron. 

Gasar ta gudana ne karkashin kulawa ta shugabannin Ittuhadus Shu'ara wanda Alhaji Mustapha Umar Baba Gadon Kaya yake Jagoranta, bisa Umarnin Jagoran Gaskiya Allama Sayyid Ibrahimul Zakzaky (H)
Taron ya kayatar matuka sosai,
 mawaqan da suka halarta sun bada kokari matuka yanda ya kamata,
 kafin gabatar da sunayen Wadanda suka zo na daya zuwa biyar an saurari jawabi daga Sheikh Muhammad Abbare, tare da wasu daga cikin manyan Alkalain da suka jagoranci shirin kamarsu Malam Bello Shehu Alkanci Talatan Mafara wanda yazo a madadin Ittuhadus shu'ara na kasa.
daganan aka gabatar da sunayen wadanda suka samu damar cin gasar sune kamar haka:
1- Umar Bakin Bege Dass - 94
2- Ahmad Deputy Gombe          93
3- Muhammad Kabir Kafin Madaki 91
4- Malam Shehu Fada 88
5- Muhammad Nasir Jos
.
Daga Wakilinmu na Bauchi
Salisu Umar Mazajen Zakzakyya

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post