SU WAYE AHLAL-BAIT (A.S) ??? (3)
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Riwaya ta gaba cikin rubutunmu na cewa;
(5)- Ibn Jarir yace, Ibn Humaid ya bamu labari, Abdullahi Bn Abdul-Quddus ya bamu labari daga A'amashu, daga Hakeem Bn Sa'ad yace;
" An ambata mana Aliyu a wajen Ummus-Salamata (R.A) sai tace;
" A cikin gidana aka saukar; " ABIN SANI KAWAI ALLAH NA NUFIN TAFIYAR DA QAZANTA NE DAGA GARE KU IYALAN GIDA.... " Sai Ummus-Salamata tace;
" Manzon Allah (S.A.W W) ya zo gidana sai yace; " KA DA KI YIWA WANI IZNIN SHIGOWA!"
Sai Fadimatu (R A) ta zo, ni kuma ba zan iya shiga tsakaninta da mahaifinta ba, sannan Hassan (R.A) ya zo, ni kuma ba zan iya hana shi shiga wajen kakansa da mahaifiyarsa ba, sannan Hussaini (R.A) ya zo, ni kuma ba zan iya shiga tsakaninsa da kakansa da mahaifiyarsa ba, sannan Aliyu (R A) ya shigo, ni kuma ba zan iya tsare shi ba.
Sannan suka hadu,sai Manzon Allah (S.A.W.W) ya lullube su da Bargon da yake kansa, sannan yace;
" WADANNAN NE IYALAN GIDANA, KA TAFIYAR MUSU DA QAZANTA, KUMA KA TSARKAKE SU TSARKAKEWA."
Sai wannan ayar ta sauko yayin da suka hadu akan shimfida." Tace;
" Sai nace, har dani yaa Ma'aikin Allah?" Tace;
" Wallahi bai amince ba. Sai yace;
" KE DAI KINA KAN NAKI ALKHAIRIN."
(6)- A wata riwayar kuma Ummus-Salamata tace; " Sai nace; " Yaa Ma'aikin Allah! Yanzu ni bani daga cikin iyalan gidanka?" Sai yace;
" KE DAI KINA KAN NAKI ALKHAIRIN, KE KINA DAGA CIKIN MATAN ANNABI NE."
Tace; " A cikin gidan, Manzon Allah ne da Aliyu da Fadimatu da Hassan da Hussaini (R.A) ."
Za mu cigaba insha Allah.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-08137925034
Tags:
Taskar ilimi