SU WAYE AHLAL-BAIT (A.S) ??? (2)

SU WAYE AHLAL-BAIT (A.S) ??? (2)



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

Cigaba:-.
A qarshen hadisi na uku da muka kawo yana cewa
" ........sai (Annabi) ya kusanto da Aliyu da Fatima ya zaunar da su a gabansa, sannan ya dora Hassan da Hussaini (A.S) akan cinyoyinsa, sa'an nan ya lullube su da mayafinsa, sannan ya karanta wannan aya;
" INNAMAH YUREEDULLAHA......" Yace;
" YAA UBANGIJI! WADANNAN NE IYALAN GIDANA, KUMA IYALAN GIDANA MAFI CANCANTA !"
(Musnad Ahmad, J:4, Sh:107)
(4)-Imam Ahmad yace, Abdullahi Bn Namir ya bamu labari, Abdul-Malik Bn Abiy Sulaiman ya bamu labari daga Ada'i Bn Abiy Rabaaha, wanda ya ji Ummus-Salama (R.A) ya bani labari yace, lalle ita (R.A) tana bada labari cewa, Annabi (S) yana cikin gidanta, sai Fadimatu (R A) ta je masa da wata Gurasa, ta shiga gare shi da shi.
Sai Manzon Allah (S) yace mata;
" KI KIRAWO MIN MIJINKI DA 'YA'YANKI."
Tace, " Sai Aliyu da Hassan da Hussaini suka zo suka shiga, suna cin Gurasa, shi kuma yana kan shimfidarsa, a qarwashinta kuma akwai wani Bargo Al-Khaibariy." Tace;
" Ni kuma ina cikin daki ina yin sallah, sai Allah me girma da daukaka ya saukar da wannan ayar; " ABIN SANI KAWAI ALLAH NA SO NE YA TAFIYAR DA QAZANTA DAGA GARE KU YAA KU IYALAN GIDA, KUMA YA TSARKAKEKU TSARKAKEWA."
Tace; "Sai Manzon Allah ya kama gefen wannan Bargo ya lullube su da shi. Sa'an nan ya fitar da hannayensa ya daga su zuwa sama! Sa'an nan yace;
" YAA UBANGIJI ! WADANNAN NE IYALAN GIDANA! YAA UBANGIJI KA TAFIYAR MUSU DA QAZANTA, KUMA KA TSARKAKE SU TSARKAKEWA!"
Tace; " Sai na fito da kaina (waje kadan) nace, nima ina tare da ku yaa Ma'aikin Allah? Sai yace;
" KE DAI KINA KAN NAKI ALKHAIRIN (na matana amma ba iyalan gidana ba ) !"
Musnad Ahmad, J:6, Sh:292
Za mu cigaba insha Allah.

Tare da Ado Isah Guda.
08126385470

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post