SU WAYE AHLAL-BAIT (A.S) ??? (1)





@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

An sami sabani game da su waye Ahlil-Bait (A S) wadanda Allah ya tsarkake su cikin Alqur'ani. Wasu suka ce matan Annabi (S) ne, wasu kuma suka ce a'a, har da 'ya'yansa (A.S), wasu kuma suka ce babu matan Annabi (S) cikin Ahlil-Bait (A.S).
Yanzu dai za mu taqaita bayaninmu ta hanyar amfani da wasu riwayoyi don sanin gaskiyar magana.
(1)- Ibn Jarir yace, Ibn Musannah ya bamu labari, Bakari Bn Yahya Bn Zaban Al-Anziy ya bamu labari, Mundili ya bamu labari daga A'amashu, daga Adiyyata, daga Abu Sa'idul-Khudriy (R A) yace, Manzon Allah (S) yace;
" WANNAN AYAR TA SAUKA NE AKAN MUTANE BIYAR; NI, DA ALIYU DA HASSAN DA HUSSAINI DA FADIMATU." " INNAMAH YUREEDULLAHU....."
(Ahzab, aya ta 33)
(2)- Imam Ahmad Bn Hambal yace;
Affan ya bamu labari, Hammad ya bamu labari, Aliyu Bn Yazid ya bamu labari daga Anas Bn Malik (R.A) yace, " Lalle Manzon Allah (S) yayi wata shida yana shudewa ta qofar Fadimatu (R A) yayin da ya fito zuwa sallar asuba, yana cewa;
" SALLAH-SALLAH YAA KU AHLUL-BAIT, ABIN SANI ALLAH NA NUFIN TAFIYAR DA QAZANTA NE DAGA GARE KU, KUMA YA TSARKAKEKU TSARKAKEWA!"
(Tuhfatul-Ahwaz, J:9, Sh:671)
(3)- Iman Ahmad yace, Muhammad Bn Mus'ab ya bamu labari, Auza'iy ya bamu labari, Shaddadu Bn Ammar ya bamu labari yace;
" Na shiga zuwa ga Wasilata Bn Asqa'a (R A), tare da shi akwai wasu jama'a. Sai aka ambaci Aliyu (R A), sai suka zage shi, sai nima na zage shi tare dasu. Yayin da suka tashi sai yace min;
" KUN ZAGI WANNAN MUTUMIN !" Sai nace, an zage shi ne shine nima na zage shi tare da su. Yace;
" Ba na ba ka labari ba game da abinda na gani game da Manzon Allah (S) ba ?" Nace eh! Yace;
" Na tafi wajen Fadimatu (R.A) na tambayeta game da Aliyu, sai tace;
" YA TAFI WAJEN MANZON ALLAH (S) ."
Sai na zauna ina jiransa, sai ga Manzon Allah (S) ya taho tare da Aliyu da Hassan da Hussaini (R.A), yana riqe da kowanne a hannunsa har ya shigo. Sai ya kusanto da Aliyu da Fadimatu ya zaunar

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post