SAKON #FREEZAKZAKY YA ISA KUNNUWAN MAHUKUNTA MUTANE DA SAURAN JAMA'A A YAU A GARIN JOS.



Kamar yadda aka sani dai duk shekara tun bayan wakiyan Zariya wanda Buhari da Buratai suka kashe Almajiran SHEIKH ZAKZAKY (H) tare da harbinsa da kuma harbin matarsa kuma a lokacin guda suka kashe wa Sheikh Zakzaky 'Ya'yansaUku don haka Almajiran Sheikh Zakzaky suke fitowa a duk lokacin da aka yi sallah EDI don nuna wa al'umma abinda akawa jagoran namu SHEIKH ZAKZAKY.

A yau ma dai Daruruwan Almajiran Sheikh Zakzaky ne suka fito babban kofar shiga Masallacin Edi na Ali-Kazaure don yin gangamin kiran gwamnatin Nigeriya data gaggauta sakin Sheikh da matarsa wanda suke tsare tsawon shekaru a hannunsu BA tare da wani ka'ida. Wannan gangamin da muke yi a kusan kowanne lokaci kullum kira muke da asaki Sheikh Zakzaky saboda rashin lafiya da yake fama da ita tsawon lokaci.

Kafin fara wannan Gangamin na #FreeZakzaky 'yan uwa Almajiran Sheikh Zakzaky sun gudanar da jawabi na Pre-Khudba a cikin Masallacin Edi wanda Malam Abubakar Sulaiman (Designer) ya jagoranta, a yayin jawabinsa yayi kira da mutane su koma bin tafarkin Allah domin yanzu mutane suna kan turba ne wanda bana Allah ba, bana MANZON ALLAH (S) ba. Don haka ma SHEIKH ZAKZAKY (H) yake kira ganin haka da kuma tona asirin kashe-kashen da ake yi a Yankunan Arewan Nigeriya su gwamnati sukayi niyyan kashe shi Amma Allah bai so ba.

A lokacin da ake yin wannan gangami mai matukan muhimmanci abin yana tasiri a zukatan Al'umman da suke wucewa, don suma zakaji yadda suke jinjinawa wannan al'amari na cigaba da tsare Sayyid Zakzaky (H) har yanzu. Abinda zai fi bawa mutum sha'awa shine,  Mu anan Jos a lokacinsu da wakiyan ta faru kowa zagi yake tare da kin tausaya mana, amma zuwa yanzu sai gashi cikin al'amarin Allah mutane sun gane menene hakikanin abin Buhari da magiya bayansa suka mana.

Gangamin anyi lafiya kalau kuma an tashi lafiya wanda 'Yan uwa da dama Maza da Mata suka samu halarta.

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates. Tare da --Idishia Jos.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post