RASHIN LAFIYAN SHEIKH ZAKZAKY HAR YANZU GWAMANATI NA NUNA HALIN KO IN KULA.



Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates, Tare da -Idishia Jos.

A labarin da ya riske mu, an tabbatar mana cewa lallai Sheikh Zakzaky ana shayar dashi da guba a inda ake tsare dashi, a lokacin da kuma jikin nashi ya kara tsanan ta na rashin lafiya. Ana cigaba da haramtacciyar tsare Sheikh Zakzaky ne bayan Umarnin da Babban Kotun Kasa ta bayar na cewa a sake shi a sake matar shi kuma a basu kulawa na rashin lafiyan da yake fama da ita tare da biyan diyya na abinda aka mai. Duk da Hukuncin da Babban Kotu tayi hakan bai hana sun cigaba da rike Sheikh Zakzaky ba.

Gwamnatin Kaduna ta cigaba da rike Sheikh Zakzaky a hannun ta inda tace tana masa wasu tuhume-tuhume wanda ya sabawa Gwamnatinsu, alhali su Gwamnatin Kasa Kotu ta bada Umarnin da cewa a sake shi suma basu sake shi ba kuma aka cigaba da haramtacciyar shari'a a kotu na Kaduna. Shekara guda kenan da fara wannan shari'a a Kaduna sai watanni Biyu baya nan  Kotu ta bada Umarnin a kula da lafiyan Sheikh Zakzaky inda aka umarci likito da zasu iya duba shi. A lokacin da likitocin suka zo daga kasar waje sun tabbatar sai dai a fita da Sheikh Zakzaky kasar waje saboda babu kayan aikin da za'a iya kula dashi a nan Nigeriya.

Sama da shekaru 3 har yanzu Gwamnatin na cigaba da tsare Sheikh Zakzaky tsarewa na jinya tare da raunuka a jikinsa. Likitoci sunyi karin bayani akan a fita dashi har zuwa yanzu shiru Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jiha sunyi murabus da wannan magana. Kuma yanzu haka an tabbatar har yanzu akwai sauran karafuna na harshashai a jikinsa da kuma idonsa guda daya, wanda idon ma ake bayani ya kusan rufewa baki daya ya daina gani dashi. Amma duk da wannan mummunan hali da yake ciki su Gwamnatin basu tausaya ma wannan bawan Allah ba.
Almajiran Sheikh Zakzaky yau a Babban masallacin Juma'a na garin Abuja a lokacin da suke gudadanar da gangamin #FreeZakzaky

Almajiran Sheikh Zakzaky a garin Abuja Kullum sai sun fito sun nuna rashin jin dadinsu na cigaba da tsare Sheikh Zakzaky ba tare da wani ka'ida ba, har ta kai ga jami'an tsaro na afkawa almajiran nashi sau da daman gaske a lokacin wannan zanga-zangan na lumana da suke yi a garin na Abuja. Baya ga nan 'Yan uwa na  garuruwa da daman gaske suma suna fitowa wannan zanga-zanga na lumana tare da Rally's a duk fadin garuruwa amma har yanzu shiru, babu alama daga ita Gwamnatin na sake shi Sheikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenatudden.

Ansha yin taron manema labarai sau da dama a na fadawa duniya halinda Jagoranmu Sheikh Zakzaky yake ciki amma har yanzu babu wani sakamako daga wajen Gwamnatin Kasar, ko a ranar Labaran satin da ya gabata anyi taron  manema labarai a cikin garin Abuja aka shelantawa duniya halinda Sheikh din yake ciki ana shayar dashi guba kuma an an 'Dasashin' Sheikh din yayi baki inda aka tabbatar guba yana tasiri a cikin jikinsa. Duniya tasha yin Allah wadai da wanna ta'addanci hatta Zanga-zanga lumana ansha yi a kasashen duniya na nuna goyon bayan su ga Sheikh Zakzaky da kin yarda da zaluncin da aka mai.

Muna kira da Babban murya da Gwamnatin Buhari data gaggauta sakin Jagoranmu Sayyid Zakzaky (H) domin a kula da lafiyansa.

#FreeZakzaky.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post