RANAR QUDUS RANANE NA TAUSAYAWA AL'UMMAN PALASTINU.



     Cewar Sheikh Adamu Tsoho Jos.

Wannan rana ta Qudus da Sayyid (H) ya aiyana ya nuna cewa babu wani mahaluki da ya isa ya rusa harka a wannan kasa ko a wannan gari, azzalumai sun sani cewa mun fito a yau domin mu nuna goyon bayan mu ga Musulmi da mutanen Palastinu da wannan Masallaci kuma insha Allah a shirya muke zamu taimaka musu ko da yaushe.

Kuma har ila yau ashirye muke zamu nuna wa wannan Jabber cewa Malam yana da 'ya'ya Harbi ko Kamu da Dauri ba zai sa mu bar tafarkin Malam (H)  ba. Kuma zamu cigaba da gwagwarmaya har sai an kawar da zalunci da azzalumai a wannan kasa dama Duniya baki daya. Allah ya nuna mana lokacin da Qudus zata dawo hannun mu, ya faranta mana rai da fitowan su Sayyid Zakzaky da matarsa.


Daga cikin Jawabin da Sheikh Adamu Tsoho Jos yayi yau a wajen rufe Muzaharar Qudus a garin Jos.

    --Idishia Jos

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post