Mu'utamar Amm@Yola 1440H 27th Shawwal 1440H (Asabar 29th June 2019)

Sheikh Adamu Tsoho Jos a wajen mu'utamar Amm


Maudhu'i: Fikirar Imam Khumaini (QS) Samuwar Harkar Musulunci karkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)

Wanda ya gabatar da Jawabi: Shaikh Adamu Tsoho Ahmad Jos

Cikin jawabinsa a wajen mu'utamar din shehin Malamin ya yi kira ga yan uwa da cewa:

1— Lallai mu sani cewa rayuwar Jagoranmu yana cikin hadari yanzu haka, kuma wajibin kowannemu, maza da mata, birni da Kauye mu farka mu fuskanci abin da ke gabanmu. Dole ne salonmu na motsi ya canza, dole ne mu motsa yan uwa, dole ne ya zama mun karfafi Muzaharori da ake yi musamman na Abuja da Kaduna. Lallai wannan hakki ne a kanmu.

2— Jagora yana da hakki a kanmu, in duk za mu yi Shahada, wallahi ba mu bawa Malam hakkinsa ba. Ba za mu iya baiwa Malam hakkinsa da ke wuyanmu ba. Saboda abin da Malam Zakzaky ya mana, in duk duniya tamu ce muka ba da rayuwarmu to ba mu biya hakkin Malam ba.

3— Kar mu manta, Malam Zakzaky ya dora mu a tafarkin Wulaya, wanda yake shine kololuwar matsayin da Allah yacewa Annabi Ibrahim mun sanya ka ka zama Imami, bayan ya zamo Annabi, ya zamo Manzo Mursali, ya zama Khalilullah, ya zama daga Ulul Azmi Minar Rusul, sannan sai Allah yace "Inna ja'iluka linnasi Imama.' Sai gashi kai wannan matsayin (riƙo da Imamancin Ahlulbait (AS) cikin sauki, albarkacin Malam Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) Allah ya dora ka a kan wannan. Wanda duk wani wanda baya tafarkin Wulaya sunanshi batacce, amma kai Allah (T) ya shiryatar da kai wannan albarkacin wannan bawa nasa. To mu ji tsoron Allah.

4— Ya kamata halin da su Malam suke ciki yanzu, su rika ji muna yin ayyuka ne na alkairi da cigabantar da Harka, dama sun mana wasiyyar cigaba da komai da ake yi. To ya kamata ya zama labarurrukan da suke zuwa ga Malam ya zama kyawawa ne ba munanan labarai, ace muna cece-kuce da juna ba. In mukai haka mun ci amanar Malam (H), kuma cin amanar Malam cin amanar Sahibul Asr Waz Zaman (AS) ne. Saboda Malam yana daga cikin babban Mu'uzijar Sahibul Asr a wannan lokacin namu, wanda har manya-manyan Maraji'ai suna nuni zuwa ga Malam. Saboda haka Allah ya mana baiwa, kar mu bari ta kubuce mana. Kuma za a tambaye mu a kan wannan baiwar da aka mana, 'Summa latus' alunna yauma izin anin na'im.' Allah zai tambaye kowa a kan wannan ni'ima da baiwa da ya mana. Don haka mu tashi mu sauke hakkin Malam.

5— Don haka zan yi amfani da wannan damar, dama mun sanar a garuruwanmu, cewa ya kamata tun daga ranar Litini (jibi) 'yan uwa a tafi Abuja. A tafi Abuja, yan uwa mu cika garin Abuja, mu yi ta Muzahara cikin kankan da kai, cikin usulbin Imam Husain (AS): "Inni lam Akruj ashran, wala badran, wala zaliman, wala mufsidan, walakin karrajtu li dalabil islahi li ummati jaddi Muhammad (S)." Yana da matukar muhimmanci lallai yi wannan, mu tafi Abuja. Abuja idon duniya ne.

6— Idan muka yi wannan cikin kankan da kai, da tawadi'u, da addu'o'i da muke yi, sai mu ga mene ne Allah zai mana hukunci da shi tsakaninmu da wadannan mutanen. Domin al'amarin gaba daya yana hannun Allah ne, amma fa sai mun tashi mun yi aiki.

7— Na san yan uwa da yawa ana kokari, amma mu kara kokari, yanzu ana maganar rayuwar Malam ne take cikin hadari. Na kan ba da misali ace ka yi sartse a jikinka ya zama ba a cire sartsen nan ba, ya kake ji? To fa Malam ba maganar sartse bane, ana maganar birbishi ne na harsasai masu guba a jikinsa, shi da iyalinsa. Baya ga sauran yan uwanmu da suke kwance.

8— Malam yana da hakki a kanmu, don haka duk abin da za mu yi ba za mu iya sauke hakkin Malam ba. Kai ba ma za iya fahimtar hakikanin Malam ba fa sai in mun je wani marhala.

9— Shahidanmu da iyalan Shahidanmu suna da hakki a kanmu. Kai al'ummar Kasar nan tana da hakki ta san wane ne Malam, meye fikirar Malam, meye da'awar Malam, daga wajenmu.

10— Yanzu ne ya kamata mu nunawa Buhari cewa Malam yana da yaya, wadanda suke a shirye suke su sadaukar da rayukansu da dukiya da mutuncinsu wajen kare lafiya da rayuwar Malam.



11— Yanzu ne ya kamata mu nunawa duniya fadin da muke cewa 'Labbaika Ya Al Zakzaky' da gaske muke yi. Mu nuna a aikace. Mu nuna cewa rayuwar Malam rayuwarmu ce, za mu iya sadaukar da komai namu a kan rayuwar Malam. Wannan kuma yana daga cikin hakkin Jagora wanda ya doru a kan mazanmu da matanmu, manya da kanana.

12— Muna fatan wadannan kalmomi da muka yi, Allah ya amfanar da mu, Ya sa mu zabura mu doru a kan wannan turba da fikira ta su Malam, wanda Allah ya musu baiwa da wannan da'awa da wannan jarabawa da suke ciki. Muna fatan Allah (T) ya bamu ikon tsayuwa da hakkin su Malam, ko da ya kai ga mu sadaukar da rayukanmu da yayanmu da dukiyarmu ne.

Daga shafin Ma'asumah Nigerian News Updates tare -Idishia Jos.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post