MUMINAI KADAI KE DAMUWA DA AL'AMARIN PALASTINAWA !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Shakka babu, kowa ya san al'ummar Palastine da ake kashewa kullum musulmi ne kuma muminai, kuma haqqi ne akan dukkan mumini ya nuna damuwarsa game da wannan halin da Palastinawa ke ciki.
Masallacin Qudus daki ne na Allah mai daraja ta uku daga cikin dakunansa dake doron qasa. Allah (T) zai iya qwato shi daga hannun wadannan Yahudawa kamar yadda ya kare 'Dakin Ka'abah mai tsarki daga garin Abraham.
Saboda haka, Qudus ba ita ce mafi muhimmanci gare mu ba kamar al'umar da ake kashewa a wannan yankin ba, domin mumini ya fi komai daraja daga dukkan wani (SHA'A'IR) na Allah in ka cire Alqur'ani mai tsarki.
Palastinawa al'umma ce musulma Ahlus-Sunnah, amma ba za ka sami masu nuna damuwarsu da halin da suke ciki ba sai dai muminai, wanda za mu iya cewa 'yan Shi'ah ne kadai suka fi nuna damuwarsu game da halin da suke ciki, alhali al'amari ne na dukkan musulmi muminai.
Allah (T) na cewa;
" ABIN SANI MUMINAI 'YAN'UWAN JUNA NE..."
(Hujrat, aya ta 10)
Sannan Manzon Allah (S) yayi magana sosai wajen nuna matsayin mumini a wajen dan'uwansa mumini. Daga ciki yake cewa;
(1)- " LALLE SHI MUMINI DAGA MA'ABUTA IMANI TAMKAR MISALIN KAI (head) NE DAGA JIKI, MUMINI NA JIN RADADI (Zogi) DA KE SAMUN MUMINI KAMAR YADDA JIKI KE JIN ZOGIN ABINDA YA SHAFI KAI (head) ."
(Musnad, J:5, Sh:340)
(2)- " MISALIN MUMINAI WAJEN QAUNAR JUNANSU, DA TAUSAYINSU, DA SADA ZUMUNCINSU, KAMAR JIKI NE GUDA 'DAYA (1), IDAN WATA GABA (part) DAGA GARE SHI TA KOKA, TO, DUKKAN JIKI NA MOTSAWA TA WAJEN RASHIN BACCI DA KUMA ZOGI."
(Bukhari, J:8, Sh:31).
Kada mu manta, duk halin da dan'uwanka ke ciki na damuwa ko farin ciki, idan ka nuna kana tare da shi ya kan ji dadi da kuma qara masa qwarin gwiwa?
To, me yasa mu ka barwa 'yan Shi'ah wannan aiki?
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
Tags:
Tunatarwa