{MUJAHADA DA SIFANTUWA DA KYAWAWAN DABI'U}

MUJAHADA DA SIFANTUWA DA KYAWAWAN DABI'U




Daga Wakiliyarmu *{Asiya A Abdussalam}*

Ibada da dabi'a mai kyau kamar Ruwa ne akan Tudu. Ita ibada matukar kana yinta tana wanke duk munanan dabi'u ne. {Misali}: Idan kofi yana dauke da Ruwa Mai launin Baki to Sai ka zubar damai Launin Bakin ka wanke kofin sannan ka zuba ruwa mai kyau: kaga kenan ka canja shi daga baki zuwa fari {Daga marar kyau zuwa mai kyau,

{MISALIN} Zuciya kenan idan ma'abocinta yana yi mata horo da niyya kyakykyawa, Dabi'a mai kyau tana matuqar tasiri azuciyar {DAN ADAM} matuqar andaure akanta sosan gaske:  Mujahada kalmar larabci ce wacce aka ciro ta daga "juhud", ma'anarsa biyu ne. Akwai 'juhud' na kokari,akwai 'juhud' na wahalar da kai domin tabbatar da wani abu. Dukkansu biyun nan suna tafiya tare ne.!
   
Kamar yadda baka wahala idan zaka yi dariya, ko kuma ka yi tafiya, tunda sun zamo maka dabi'a, shi ya sa basu baka wahala, haka al'amarin mujahada ma yake. Da mujahada ne mutum zai samu kusanci ga Allah na musamman, Wanda zai zama Allah ne mai lura da ayyukanshi gaba daya. Akwai wasu abubuwa guda biyu wadanda ake samu ta bangaren mujahada, sune: 

{Kamar Haka::} Ilimi(,Wanda ya zo daga Allah)' Sannan akwai wani abu Wanda Allah ne ke sa maka a zuciyar ka Wanda duk abinda ya taso kana yi masa kallo a hakikanin da yake. Har ma Allah (T) yana cewa " fattakullaha wa yu allimukumullah", ma'ana ku yi takawa shi kuma Allah ya sanar da ku.
Da ibada ne Allah zai so ka, idan Allah ya so ka, zai zamo jin ka, ya zamo ganin ka, tafiyar ka, da duk aikin ka. Zaka kaucewa muguwar cutar son rai. Allah kada ka sa mu zamto daga cikin masu cutar son rai bi hakki fatima wa abiha. {A.s}

Daga wakiliyarmu *{Asiya A Abdussalam}*
   

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post