Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates Tare da -Idishia Jos.
Bayan Harin Ta'addanci na Mahara Yan Bindiga A ranar Jumu'a a garin Faru dake Cikin karamar Hukumar Maradun Wanda Yayi Sanadiyyar Rasa Rayuka akalla Biyar tare da Jikka Wasu.
Wakilin Yan Uwa na Faru Malam Abubakar Ya Rasa Rayuwarsa a jiya Asabar bayan Jinya ta kwana daya Sanadiyyar Harbin da Yan bindigar Sukayi Masa.
Wakilin Yan Uwa Na Faru Malam Abubakar Faru cikin Sahun Muzaharar Free ZAKZAKY shekaran jiya Jumu'a a garin Talatar Mafara Kwana daya Kafin Mahara Su kasheshi Yau Assabar a garin Faru dake Cikin Karamar Hukumar Mulki ta Maradun a Jahar Zamfara.
Bihar Zamfara dai tana shan fama da hare-haren 'yan ta'adda da sunan barayin shanu wanda ya kai ga kusan kullum sai anyi asarar rayuka masu yawan gaske. Tun a shekarun baya Sheikh Zakzaky (H) ya bayya wannan ta'addanci BA komai bane illa kwasan dukiya da turawa keyi a wajen. Don haka sai an shafe mutanen wajen sannan a samu daman diban dukiya.
#FreeZakzaky
Tags:
Labaran Duniya