KOKUNSAN ABUBUWAN DAKE KARA KAUNA TSAKANIN MIJI DA MATA???

KOKUNSAN ABUBUWAN DAKE KARA KAUNA TSAKANIN MIJI DA MATA???



Cikin Hikimar Allah daya sanya zaman takewar Aure ta zamo tsakanin namiji da mace, baisa namiji ya auri namiji ba kuma baisa mace ta auri mace ba:

Bisa shari'a namiji shike auran mace to yana da kyau musan wanene namiji?
Namiji halittar Allah ne mai daraja halittar sa da dabi'ar sa ya ban banta dana mace hakama kaifin tunaninsa da hangen nesan sa Ya dara da kwakwalwar mace kamar yadda Allah ya fada a cikin alkur'ani  Mai Girma:

"ARRIJALU KAUWAMUNA ALAN-NISA'I..."
Namiji yana da kaushin dabi'a da murya yana da kaifin hankali da jarumta shine mai nemo dukkan abinda iyalinsa zasuyi amfani dashi yana da karancin hakuri wurin rainon yara da rike wasu al'amura na tsakar gida.


Namiji shine gatan mace a matsayinsa na da ko miji ko kuma mahaifi, domin kuwa idan mace ta rasa daya daga cikin uku nan to rayuwarta sai Ta sauya.


Kafin aure ya kamata ace mun lura da wasu ka'idoji kamar tabbatar da kauna tsakanin namiji da mace don itace asasin zaman aure saboda in babu kauna tsakanin ma aurata to bazasu tausaya wa juna ba:


Dole a samu fahimtar juna don gina sabuwar rayuwa domin asami kyakkyawan gida mai tsari Wanda bayin Allah salihai zasu fito daga cikin sa:


Wani bature mutumin America yace kafin suyi aure da matarsa sai da tayi masa tambayoyi kimanin 400 arubuce kuma ta fada masa unguwar da take son ta zauna saboda bata son hayaniya da kuma inda take son zuwa yawon shakatawa d.s.s:


Sannan akwai wani bature mai suna John dorn da yake magana game da ra'ayinsa akan aure cewa yayi aure shine cikar kamala Wanda yake baiwa mutum aikinyi domin koda yaushe yana tunanin akwai Wanda yake neman wasu abubuwa na bukatun rayuwa a wajensa:


Idan muka duba zamuga cewa su ba musulmai bane Amman kuma suna yima zaman aure tanadi to mu kuma musulmai da da ta kasance sunnar Manzon Allah (S) muke to wane irin tanadi mukayi ma tamu rayuwar auran???

Masana sun tabbatar da cewa ba'a taba samun wani aure mai tsari Wanda akayi da kyakkyawar niyya kamar Auran Soyayyah Da Qauna Ba,  Allah Ka Azurtamu da Mazaje Na Gari Masu Sonmu Domin Allah Da Manzan Sa (S)

Nan Zamu Dasa Aya Saikuma Mun Hadu A Kashi Na Biyu Insha Allah Allah Ya Datar Damu, !

Daga Waliyarmu *(Sakina Ahmad Kazaure)*
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post