KAMAR SAURAN BIRANE A NIGERIA SAKKWATO MA AN GUDANAR DA MUZAHARA QUDUS.
Mas'ud Dan Masani Shinkafi
Ishaq Muh'd Suleiman
à yau juma'ar ƙarshen watan Ramadan Ƴan Uwa musulmi mabiya Mazhabar Shi'a a Nigeria almajirin Sheikh Ibraheem Yaqoub El Zakzaky sun gudanar da Muzaharar Qudus domin jaje ga al'ummar Palestine Raunana bisa zaluncin da ake musu shekara da Shekaru da ƙin yadda da cigaba da ƙwace masallaci na uku mafi daraja da Yahudawan Sahayoniya Isra'ila sukayi suka maida shi wajen aikata ɓarna da fasidi, sama da shekaru 60 da kafa wannan haramtacciyar ƙasa wanda aka kafa bisa bisa zalunci da ƙin jinin musulunci.
An dai fara ita wannan Muzaharar ne daga titin Sultan Dasuki Road anan babban birnin Sokoto aka bi ta Sultan Abubakar Road aka bi ta Bauchi Road aka wuce Zaria Road aka kuma bi ta unguwar rogo round about,
Muzaharar dai ta kwashe kusan kusan awa biyu da Ƴan kamar mintuna arba'in,
Wakilan Ma'asumah Nigeria News Update mun zanta da ɗaya daga cikin masu gabatar da wannan Muzaharar a daidai lokacin da aka zo Bauchi Road ga nan yadda hirar mu ta kasance dashi.
""
Ma'asumah:- Malam Sannu, ko zamu san me kuke yi haka?
..... Eh muna yin muzaharar Qudus domin nuna goyon bayan mu ga al'ummar. Falasdinawa kamar yadda muka saba sama da shekaru 25,
Maasumah :- meye manufar wannan fitowar taku?
..... Manufar fitowar mu shine domin nuna rashin amincewa da wannan zaluncin da akewa Raunanan musulmin Palestine da kuma kiran a Dakatar da zubar da jininsu,
Ma'asumah:- Meyasa a wasu lokuta idan wannan zanga zangar lumana akan samu rikici wanda hakan yakan kai ga a sarar rayuka ko mummunan rauni?
..... :- kamar yadda na gaya maka wannan Muzaharar dai ta lumana ce saboda mu bama takalar kowa kawai muna isar da sakon dalilin fituwar mu ne domin idan ka lura ba wanda yake riƙe da ko allura da sunan makami, amma se asamu wasu da basa so mu bayyana ra'ayin mu ko muyi Addini yadda muku fahimta suzo su kawo manna hari ko suyi yunkurin kawo cikas ga abinda muke,
Ma'asumah:- idan haka ne meyasa bazaku daina ba?
..... :- Eh bazai yiwu bane saboda ba'a daina Addini wai saboda wani bayaso ayi tausayawa falasdinawa Addini koba komai akwai kishin Masjidus Al'aqsa cikin Tausaya musu ɗin.
Ma'asumah :- wasu mutane na cewa to ai bama Nigeria wannan abun ke faruwa ba to ku meye naku na damuwa?
.... :- kamar yadda ka sani mu muna yin wannan Muzaharar ne da sunan Addini, tausayawa Ɗan Uwanka Musulmi Addini ne, kuma Sayyid Zakzaky (H) yana kiran mu ne ga Addinin Allah kacokaf ɗinsa ba tare da ware wani abu ba, Manzon Allah Yace:- wanda duk ya wayi gari be damu da Al'amarin Musulmai ba to baya daga cikin mu.
Ma'asumah :- Insha Allah mungode kana tare da Ma'asumah Nigerian News Update
.... :- Muhammad Ahmad Sokoto Insha Allah.
Ƙarshen rahoton namu kenan
Ishaq Muh'd Suleiman
Mas'ud Dan Masani Shinkafi
Tags:
Labaran Duniya