HARIN SOJOJI AKAN MASU MUZAHARAR FREE ZAKZAKY A KADUNA.

                                                     
Gungun Sojoji dauke da kayan yaki, sun dirarma 'yan shi'ah Masu Muzaharar FreeZakzaky a Kaduna da yammacin jiya Asabar 08/06/2019 a tsakiyar garin na Kaduna.

Lamarin ya aukune a shatale talen Gwamna Road, bayan fara Muzaharar da misalin karfe 6:00pm sai ga wucewar tawagar wani babba daga cikin 'yan siyasar kasarnan, Harisawa sunyi kokarin samar masa da hanyar wucewa, inda ya wuce ba tare da wani fargaba ko razanarwa ba.

Masu Muzaharar sun isa Askwalaye (by fast) kawai saiga tawagar gungun Sojojin Nigeria, suna isowa suka fara budewa Al'umma wuta da rana tsaka sun harbi mutum 2 a cikin 'yan Uwa kuma Al'ummar gari sun shaidi yadda lamarin ya auku sunyi Allah wadai da wannan harin na zalunci kan wadanda basu dauke da komi a hannunsu.

Zuwa hada wannan rohoto babu tabbacin samun Shahidi sai dai masu raunuka kuma munana.
___________________________________________________
Wakilan mu na Kaduna:
__________________________
AMR UMR da FTM Zahra Shi'it
—09/06/2019

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post