-Cewar Sheikh Adamu Tsoho Jos.
Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Updates tare da -Idishia Jos.
Ba komai zaka dauko kayi posting din shi ba, ba komai zaka rutuba kayi posting din shi ba,komai yana da muhallinsa komai yana da lokacin sa, asan me ya kamata a rubuta asan me ya kamata a yi posting. Ya zama babban abinda zaku bada mahimmanci ya zama karfafa 'yan uwa akan harka da fadada fikiran 'yan uwa su tsaya akan fikira salimiya wacce Malam (H) ya Dora 'yan uwa a kai, karfafa 'yan uwa da zaburantar da 'yan uwa akan jajircewa da tsayuwa akan harka musulunci Tsarkaka 'yan uwa akan sada zumunci da karfafa 'yan uwa akan Muzahararori da Rally's da ake yi da duk wani abu da ake yi na ganin su Malam sun fito, wannan yana daga cikin bigiren abinda za'a mahimmantar domin a zaburantar da 'yan uwa.
Duk abinda zai kawo rarraba a gamana ko a aiki dan Media ne ko ba dan media ba to wannan cin amanan harka ne, abinda ya zamo wajibi akan mu shine Mu tsayu akan abinda zai hada kammu, ta yadda al'umma suke ganin mu da wannan kima ya zamo sun kara ganin mu fiye da haka. Ta yadda zai zamo soyayya mu da 'yan uwantakan mu da haduwan mu da samun wahada a cikin mu, da ayyuka da zasu gani a cikin mu kyawawa na gaskiya da amana da cikin alkawari ya sanya sun karkato sun fahimci wannan da'awa na Malam (H). Don haka ya kamata kowanne mu ya zama Malam ne a inda ya samu kansa, mutane suga gaskiya su amintar da kai su ga amanan ka su ga " makarimul aklak " din ka wannan shine da'awa da abinda ake bukata.
To ta wajen rubutu ma akwai wannan ya zamo cewa mutum ya inganta rubutunsa ba kawai zai yi rubutunda mutane zasuyita Allah wadai ko rubutunda zai kawa zato ko rauni, da raunana imamin 'yan uwa ko rubutunda zai kawo abinda zai sa yan uwa ba zasu zabura ba, in wajen infaki ne ba zasu bayar ba, in wajen fitowa muzahararori ne ba zasu fito ba, to wannan kaga in mutum yayi yaci amanan harka ne yaci amanan su malam ne. Muyi abinda zai karfafa jajircewa a tsakanin mu don gamin su Malam sun fito daga hannun azzalumai, to wannan suna daga cikin muhimman al'amura wanda ya kamata ace mun lura dasu a wannan marhala din.
MUSAMMAN wajen posting abubuwa da ya kamata ace su 'yan Media suna la'akari da posting muhimmai tunda yanzu yanki-yanki ne ana da 'yan Media na yankuna ya kamata a dunga la'akari da rubutu muhimmi wanda zai kawo ma harka cigaba, ya ilmantar, ya wayantar da kan 'yan uwa ya zaburantar da 'yan uwa a inda ka samu kanka, ba kawai ka yi linking ba, idan kaga posting ba wai liking posting ake so ba, ya zama muhimmi sai kayi sharing ta yadda yake duk wani friend din ka idan kayi sharing zasu gani, amma in kayi liking wanda yayi post din ne kawai zai gani, amma lokacin da kayi sharing al'umma da dama ne zasu amfana wannan sai ya zama ba kai ne kayi posting din ba amma kayi "Tabligi" zaka samu ladan kamar kaine kayi rubutun.
Akwai jawaban su Malam (H) Audio ne ko Video, ya kamata muna posting jawaban su Malam saboda mutane suji bayanai nasu Malam (H) suji daga su Malam (H). Sannan akwai wasu daidaikun jawabai na Almajiran su Malam mai muhimmanci to kaga shima babu laifi sai ayi sharing, ya zamo muhimmi ya zamo abinda zai amfanar da 'yan harka. Musan cewa duk abinda zamuyi post ko share ya zamo ZAI amfamr da mune ya kuma amfani suma al'umma din ya zamo cigaba ne na gini akan abinda Malam (H) yake ginawa ba rusawa ba ba zagon kasa ba, ba bukatan tsegumi ko gulman wani ko yada zato, idan kaga dan uwanka yayi kuskure ba'a social media ake yadawa ba.
Social Media wajen nasihane da wa'azi kuma ba'a kama sunan mutum, ba'ayin wani abu da zai nuna kana magana da wane ne, manufar shine addini Nasihane ga Allah da Manzon Allah (S) da sauransu har ga al'umma musulmai nasihane. Saboda haka idan dan uwanka yayi kuskure to same shi kaje ka gyara mishi kai dashi in zaka iya. Amma in zai zamo 'yan uwan mu suyi kuskure ya zama zamu shiga social media ne wai zamu gyara musu to wannan barna ne da zagon kasa. Musan cewa duk abinda muka yi akwai ranar da za'a tambaye mu akai. Allah yana cewa;- Wallahi na rantse da ubangiji ka ya Muhammad wallahi sai mun tambaye su 'Zamu tambayesu dukkansu Baki daya' dangane da abinda suke aikatawa.
Idan kayi posting alkhairi zakaga alkhairi, idan kayi posting shairi to zakagan sakamakon Sharrin ka, wani lokaci social media yakan shagaltar damu yasa mutum yaita abubuwa daban-daban, to ka sani kai Mas'ul ne kowanne mutum da ya samu kansa a harka nan akwai bangare da ya zama shi mai kiwo ne a wannan bangare kuma za'a tambaye shi a wannan bangare. Sabida haka a matsayin ku na 'yan media ku sani za'a tambaye ku duk abinda kuka yi posting ko Sharing sai Allah ya tambaye ka. Fatan mu Allah yasa muyi aiki na sauke nauyin da yake kammu dangane da wannan da'awa da Malam (H) da sauran al'umma baki daya.
#FreeZakzaky
Tags:
Tunatarwa