DARUSA DAGA RAYUWAR SAYYID ZAKZAKY (H) !!! (2)
Daga Wakilinmu
(Ado Isah Guda)
08126385470-08137925034
Cigaba daga rubutun mu na baya shine;
(5)-DAKEWA:- Ya kasance babban matakin nasara dakewarka kan abinda kake yi. Duk wani me da'awar dawowa kan tafarkin gaskiya, to, dole yaci karo da jinsin mutane uku, wato, Azzalumai, mahassada da kuma munafukai.
Duk wadannan za su taru a kansa don daqile abinda yake kira a kansa.
Shine Allah (T) ke cewa;
" KA TSAYA QYAM KAMAR YADDA AKA UMARCE KA."
To, Sayyid (H) ya tsaya qyam kan wannan kira nasa duk da cewa ana yunqurin ganin bayansa, amma hakan ba ta sa ya canza ba.
Saboda haka ya kasance makwafi/madubi gare mu wajen koyi, domin shine ke fassara mana haqiqanin da'awar Manzon Allah (S.A.W.W).
(6)-GASKIYA:- Yana da gaskiya a zantukansa da ayyukansa, domin ba ya cin amana, kuma bai taba yin magana ta son ransa ba wacce kan iya janyo masa qasqanci in ya canzata daga baya ba.
Ina iya bugun qirji nace, in akwai guri daya (1) tak wanda ya taba yin wata magana wacce daga baya ya canzata, to, a kawo min ! Hakan ya taimaka wajen ba shi kariya daga sukan 'yan adawa.
Wannan ita ce babbar siffa ta Annabawa da Manzanni (A.S) da kuma magadansu na gaskiya.
Shi yasa ba na jin kunya ko tsoro wajen bayyana kaina cewa ni 'DAN SHI'AH ne kuma mabiyinsa (H), domin ba shi da abin suka a rayuwarsa, sai dai irin hassadar nan ta munafukai da fajirai wacce suke yiwa Manzanni (A.S) da Mujaddai.
Daga Wakilinmu
(Ado Isah Guda)
08126385470-08137925034
FREE SAYYID ZAKZAKY (H) !!!
Tags:
Tunatarwa