DARUSA DAGA RAYUWAR SAYYID ZAKZAKY (H) !!! KASHI NA(1)
DAGA WAKILINMU
(MALAM Ado Isah Guda.)
(MALAM Ado Isah Guda.)
(08126385470-08137925034)
Cikin rayuwar Sayyid Zakzaky (H) akwai darusa kamar haka:-
(1)-KYAUTATA TARBIYYA:- Sayyid (H) ya taso da kyakkyawar tarbiyya abin koyi gare mu, tun daga halin quruciyarsa har zuwa wannan lokaci da muke ciki Wannan ya taimaka matuqa wajen samun kariya daga dukkan wasu qalubale da zai iya fuskanta daga jahiliyya, miyagun malamai da kuma abokan zama da za su iya kawowa don sukar sa.
(2)-ILIMI:- Shine babban jigo wanda mutum zai dogara da shi wajen isar da saqo Sayyid (H) ya kasance masani cikin dukkan ayyukansa da zantukansa. Shi yasa yake cewa;
" ILIMI SHINE BABBAN MAKAMI/QARFI A WANNAN ZAMANI NA YAQAR MAQIYA, QARFI BA YA IKO TA WANNAN JANIBI!"
Ya bada misali da professor da mai faskaren itace, yace;
" IN DA FADA ZA AYI A TSAKANINSU WA KUKE GANI ZAI BUGE WANI? AMMA YANZU ILIMI SHINE QARFI ABIN TINQAHO."
(3)-TSARKAKE AIKI:- Ya kasance dukkan ayyukansa ya kan yi su ne don Allah da kuma neman yardarsa. Ba ya buqata ka yabe shi ko kuma tsoron kada ka zage shi cikin ayyukansa, sannan ba ya zargin wani don ya gaza a aiki, burinsa kawai shine ayi don Allah ba don neman suna ba.
(4)-TAIMAKO:- Wajen taimako ba ya nuna bambanci tsakanin mabiyansa da kuma wadanda ke kan wata fahinta ta dabam.
Wannan dalili yasa kiristoci su ke yi masa kyakkyawar fahinta da kuma gamsuwa da da'awarsa Za mu iya fahintar haka ta bangaren rabon kayan masarufi na azumi, yawancin wadanda ake ba su (beneficiaries) din ba 'yan'uwa bane. Yin hakan kuwa ya kasance wata babbar hanya ta isar da saqo, domin dukkan rai tana son mai kyautata mata.
Za mu cigaba insha Allah
DAGA WAKILINMU
(MALAM Ado Isah Guda.)
DAGA WAKILINMU
(MALAM Ado Isah Guda.)
(08126385470-08137925034)
Tags:
Tunatarwa