*BUHARI NA WASA DA LAFIYAR SHAIKH ZAKZAKY*
Daga Wakilinmu
(Zaidu Suleiman Shi'a)
A ranar Juma’a 21/06/2019 waki’ar kisan kiyashin da gwamnatin Buhari ta yi ga Shaikh Zakzaky da jama’arsa ta cika watanni 42 da kwana 10 a lissafin Miladiyya. Ta’addancin da ya fara a ranar Asabar 12/12/2015.
Tun sannan ba mu gushe ba muna fitowa daga lokaci zuwa lokaci muna muzaharar lumana don tunawa jama’a irin bakin zaluncin da aka yi wa Jagoranmu Shaikh Zakzaky, tare da yin kira ga gwamnatin da take tsare da shi ba bisa hakki ba, da ta sake shi cikin gaggawa, ba tare da wani sharadi ba.
Sanin kowa ne cewa, har ya zuwa yau din nan da muka sake fitowa, gwamnatin Buhari ba ta bi umurnin wata babbar kotun Abuja da ta ce a sake shi ba, har ma a biya shi diyya, shi da mai dakinsa Malama Zeenah Ibrahim. Tunda ko haka ne, hakarmu ba ta cimma ruwa ba kawo yanzu, to ba za mu yi kasa a gwiwa ba, za mu ci gaba da fitowa don jaddada bukatunmu da sake tunatar da jama’a.
A wannan karon hankalinmu ya kara tashi ne saboda yadda rashin lafiyar Jagoranmu Shaikh Zakzaky ke kara tabarbarewa a kullum, saboda burbushin harsashin da ke jikinsu da kuma guban da ke tattare da harsasan. Sanin kowa ne cewa wasu kwararrun Likitoci da suka zo daga kasashen waje tare da hadin gwiwar Likitocin gwamnati sun duba lafiyar Jagoran namu da matarsa, kuma sun ba da sanarwar cewa suna bukatar kulawar gaggawa a Asibitin kwararru wanda samun sa sai a kasashen waje. Kawo yanzu dai ba wata alama da ke nuna gwamnati ta yi wani abu kan wannan rahoto na Likitoci.
Ko ba mu fada ba, duk wani mai hankali ya san cewa, gwamnatin Buhari tana jan kafa ne a kan wannan bukata tamu ta sakin Jagoranmu Shaikh Zakzaky da burin ko ta Allah ta kasance da shi (wa iyazu billah). Amma ganin yadda tsohon Shugaban Misira, kuma daya daga cikin jagororin kungiyar masu kishin Musulunci ta Ikhwanul Muslimun, wato Muhammad Mursi, ya rasu yana tsare a hannun azzaluman mahukuntan Misira, hankalinmu ya kara tashi, kuma damuwarmu da halin da Jagoranmu ke ciki takaru.
Zai zama katon kuskure idan mahukuntan Nijeriya da ma sauran azzaluman mahukunta irin na Misra, za su yi zaton idan wani wanda suke tsare da shi ya rasu a hannunsu, babu hannunsu a ciki. Wannan zaton da suke yi ba mai karbuwa ba ne a mizanin hankali da ma shari’a. Ya za a yi kuna tsare da bawan Allah, kun hana shi damar ya je ya kula da lafiyarsa yadda ta dace, sannan ya rasu, ku ce ba laifinku ba ne, mutuwar karar kwana ce, lokacinsa ne ya yi? Sanin kowa ne cewa ba haka ake mutuwar karar kwana ba.
Tun farkon wannan waki’a ta kisan kiyashin Zariya a 2015, mun san cewa wannan gwamnatin ta Buhari ta fito da karfinta ne don ta kashe Jagoranmu Shaikh Zakzaky da jama’arsa, Allah ne kawai ya cece shi daga hannunsu, ba don suna so ba. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da ba Jagoran namu kariya daga sharrin makiyansa a wannan karon da suke tunanin sannu a hankali ta Allah za ta kasance tare da shi. Duk da haka muna son su sani ba za mu lamunci wannan dabara ba ta kisan mummuke. Ba fa za mu zura ido kawai karin wani mummunan abu ya samu Jagoranmu ba, don kuwa mun san wadanda suke da alhakin haka, kuma kansu za mu dora alhakin.
Don haka muna kara kira ga duk wani mai yi wa kasar nan fata na gari da ya ja hankulan azzaluman mahukuntan kasar nan kan gurguwar dabarar da suka dauka ta ci gaba da tsare Jagoranmu Shaikh Zakzaky da sauran ’yan’uwa bisa uzurin cewa yana fuskantar shari’a a wata kotun jeka-na-yi-ka ta jihar Kaduna. Karrr muke kallon su! Mun ki wayon! Ku sakar mana Jagoranmu kawai! Ba ku da wani uzuri na kin yin hakan da gaggawa!
SA HANNU:
SHAIKH ABDULHAMID BELLO ZARIYA
21/06/2019

Tags:
#FREE_ZAKZAKY