AUREN WATA SISTER. kashi na karshe. HASSAN YA AURI ZAINAB BURIN 'YAN HARKA AUREN DAN UWA DA 'YAR UWA.



Babban abin farin ciki a wajen iyayen Zainab Allah ya bawa 'Yar su dan uwa wanda yake da wulaya ga A'immatu Ahlulbait (As), cikekken Almajirin Sayyid Zakzaky (H) ba ba'ame ba. A ranar da aka zo daurin aure a lokacin da kowa-da-kowa ya halacci taron 'yan uwa, dangi, abokanan babanta da abokanan Baban ango an cika, angon kuma yasa Shadda shi mai tsada "Sky Blue" tare da abokansa kowa baki ya kasa rufuwa sai farin ciki ake. Manyan Malamai sun zo daga sassan garuruwa duk don albarkancin harka Islamiyya, kafin isowan wakilanta da wakilansa an fara gabatar da jawabi ne a wajen  akan falala da daraja na aure musamman ma ace kana da 'ya ta auri ma'abocin addini wanda yake bai damu da komai ba sai Ganin tabbatan Addinin Allah, sabanin auren da ba dan uwa zata aura ba, wanda Addinin nasa ma bai sani ba balle kiyaye dokoki da shari'a ta Addinin Ba'ame kenan.

Wakilan Hassan sun karaso aka fara gabatar da daurin auren a gaban babban wani Hujjatul Islam, kuma ya gansu da yadda aka bada aure da duk abinda aka yi, a nan ne aka yi addu'oi aka watse aka shafa Fatiha. Abokanan Hassan fa sai murna daya daga cikin su yayi Salawat mai karfi Gaske sai duka aka ga sun tsuguna tare da salatin Annabi (S) da iyalan Gidansa don girmamawa. Dagowanda suka yi aka fara Hotuna ta ko ina, daga nan aka wuce "Chinese Garden" domin walima an cika ta ko ina an dauko Amarya Zainab a mota tare da kawayen ta. Daman an gayyaci Malamai suma daga wajen daurin auren suka zo wajen waliman, suka yi jawabai masu sanyaya rai musamman ga sauran Matasan da basuyi aure ba abin ya basu sha'awan Ina ma ace wannan ranar sune, kuma aka kwadaitar dasu auren Sister ba Ba'amiya ba kamar yadda Sayyid Zakzaky (H) yasha fada. Kabbara kawai kake ji da Salawat, su kuwa ango da amarya suna kan "High Table" kai a sunkuye musamman ma dai ita amaryan.

Anyi biki lafiya kalau kowa ya koma gida da murna, iyayen ango da amarya sun musu nasiha sosai da kula da hakkin aure musamman ma Ita amarya da ta kiyaye yin wasu abubuwa da aikata muhimman abubuwa a gidan miji.  abokan ango sun raka ango dakin amaryansa, sun musu nasiha dai-dai gwargwadonsu, suka juya suka tafi. Anyi auren Ranar Juma'a ranar Monday da safe sai ga kiran waya Zainab ta dauka tayi sallama aka tambayeta kece Zainab! Tace a nice dawa nake magana ? Sai yace mata wani bawan Allah ne almajirin Sayyid (H) ya bada sunan Ki da sunan Mijinki ya biya muku karatu fita kasar Iran kyauta shine yace a sanar muku. Zainab tace Masha Allah suna godiya amma zata bashi number mijinta suyi magana dashi kai tsaye! Yace ba matsala hakan. Ashe wanda ya biya musu kudin karatun da Zaman su a can wani abokin Baban Zainab ne  wanda suka taso tun suna yarinta amma shi Allah ya azurtashi da arziki mai yawan gaske.

Shirin tafiya kasar waje yayi nisa, a ranar da 'Visa' su ya fito sunyi murna da karin godiya ga Allah. Ana washe garin tafiyansu Baban Hassan da Baban Amarya Zainab da iyayensu mata sunzo gidan Hassan din, suka musu nasihohi da jankunne da kiyaye hakkin Aurensu idan sun tafi, shikke nan kuma ranar Litinin aka rakasu filing Jirgin Malam Aminu Kano suka tafi. Sun shafe awanni a jirgin kafin saukan su, bayan sun sauka kuwa sun tarar da masu tarban su aka kaisu masaukinsu a matsayin su na mata da miji. Shi Hassan ya fara karatu ne a bangaren Chemical Engineering ita kuma tana karantar likitanci ne. Shekarunsu kusan Uku basu dawo gida Nigeria ba har Allah ya Azurtasu da haihuwa yaro namiji suka samai suna Haidar Aliyu kenan. Sun dawo Nigeria ganin gida kafin su koma yaronsu har ya fara rarrafe yana kokarin tafiya, iyaye sai farin ciki duk da yake hutun wata daya kawai suka samu zasu koma kuma.

Haka dai lokaci yayi suka koma har suka kammala karatun su baki daya Hassan ya fito da sakamako mai kyau a makarantar duk da yake yasha wahalan gaske wajen karatu da rashin bacci don takardansa yayi kyau. Ita kuwa Zainab daman wajen karatu ba'a magana ganin kokarin tane ma abokin Baban ta ya biya musu tafiya Janhuriyar Musulunci ta Iran, ita ma Allah yasa ta fito da First Class Upper bada tarin kyaututuka da suka samu. Da suka dawo gida Nigeriya, kowa ya samu aikin gwamnati a cikin su. Harma makarantar su na Iran sun basu daman idan suna so su zauna a can zasu dauke musu nauyin komai banda salary su da za'a na biyansu amma Zainab ta matsa sai dai su dawo gida Nigeriya suyi aiki. Tunanin Zainab shine abin yana bata takaici akai mace asibiti Maza suna aiki a kanta ina ma ace a NIGERIYA mata likitoci za'a ware musu asibitin su daban ana kai musu jinyan mata 'yan uwansu suna kula dasu har mace ta samu lafiya!.

Labarin Zainab kenan wanda na yi mai lakabi da AUREN WATA SISTER, Anan kuma zan dasa Aya na a cikin littafi kashi na Daya (1) sai in Allah ya kai mu wani lokaci zamu zo muku da sabon labari na daban Ina fatan duk wanda ya amfanu da wannan labari yayi salati ga Annabi (S) da Iyalan gidansa tsarkaka.

Bissalam naku --Idishia Jos.

#FreeZakzaky

2 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Ikon Allah.

    Allah sarki.

    Ku ziyarci shafinmu na yanar gizo domin karanta labarai, rahotanni, dauko wakokizlitattafai da sauransu.

    🌐 HausaeDown.com.ng</a..

    ReplyDelete
Previous Post Next Post