KOKUNSAN CEWA ANNABI ISAH (A.S) YA BADA LABARIN SAYYID ZAKZAKY (H) A KARSHEN ZAMANI ???*


*KOKUNSAN CEWA ANNABI ISAH (A.S) YA BADA LABARIN SAYYID ZAKZAKY (H) A KARSHEN ZAMANI ???*

Daga MSRa’is Funtua.



*Zuwa ga Abokina Mr Kirista a cikin son Adalci da ‘yan Adamtaka.*

Tun bayan wannan waki’ar 12/12/2015 nake ta kokarin naga na wayar maka dakai akan jagorana wanda ake ta wahalarwa cikin zaluntarsa daga masu mulkin Nijeriya.

Wanda aka tsorataka akansa alhali shi yana daga cikin amintattun bayin Allah nagartattu masu son kawo gyara a cikin jama’ar Ubangiji da kullum kake kadaita shi Allah da cewa Haliluya(La’ilaha illallah). Ayau naso ne nayi tsokaci a cikin littafin Annabi Ishaya, domin ku gane mani hanya akan fahimta ta danayi ma Littafin na Annabi Ishaya.


Bari na fara da tuna maka abinda ka sani cewa Annabi Ishaya (A) ya rayu a tsakanin shekaru dari 8 zuwa shekaru dari 7 kafin haihuwar Annabi Isa (A). Littafin Annabi Ishaya(Isaiah) alaihis salam, Littafi ne da yazo a cikin Littafin Tsohon Alkawari (Old Testament) Litafin yana da Babi guda 66.


Sannan kuma aka tattarashi a cikin ayoyi 1292. Littafin na Ishaya littafi ne da ya shahara wajen bayar da labaran al’amuran da zasu faru a karshen zamani har ya zuwa al’amarin baiyanar Imam Mahdi (A) da kuma alamomin baiyanar gami da wasu daga cikin waki’o’in da zasu faru a wasu Kasashe kafin biyanar ta Imam Mahdi(A):


(kamar Iraki da Masar, Siriya, Habasha Da sauransu.)


A cikin Babi na 52 da kuma babi na 53 na Littafin, Annabi Ishaya ya ambaci labarin wani zababben bawan Allah da zai sha wahala ta dalilin neman ceton jama’arsa alokacin da za ayi yinkurin kashe shi. Amma daga karshe ikon gudanar da al’amura zai komo a hannunsa domin bayin Allah talakawa su sami ‘yanci:


Labarin ya fara ne kamar yanda na ambata daga aya ta 13 na babi na 52 da yake da ayoyi 15 sai aka kammala bayar da labarin a cikin babi na 53 da yake da ayoyi 12.Wannan waki’ar da tazo wa Saiyid Zakzaky da wahalarwa ta kasance a lokacin yana da shekaru 65 a duniya. Kamar yanda labarin ya fara daga Babi na 52 aya ta 13 ( 52 + 13 ) = 65:


Domin an haifi Sayyid Zakzaky ne a shekara hijira ta 1372 waki’ar tazo a shekarar hijira ta 1437,(1437-1372)=65.
Ga dukkan manazarci akan al’amarin ita wannan waki’ar in ya bibiyi wadannan ayoyin 15 zai ga tabbas kamar ana bamu labarin lamarin Sayyid Zakzaky ne a cikin wannan waki’ar da ta fara a ranar 12/12/2015. Da kuma yanda karshen lamari zai kasance a tare da Sayyid Zakzaky:


Yanzu bari mubi wadannan ayoyin dan muga ko tunanin da nake da shi akan wadannan ayoyin ko sun iya alakantuwa da su Sayyid Zakzaky?


Bari mu gani dan hankalinmu ya zame mana alkali. Annabi Ishaya ya fara da cewa:


*Bawan Ubangiji Mafi Shan Wuya (a Nijeriya saboda ra’ayinsa)*
*Ishaya 52:13.Ubangiji ya ce, “Bawana zai yi nasara a aikinsa, Zai zama babba, a kuwa girmama shi ƙwarai.*



Hakika Saiyid Zakzaky tun daga faruwar wannan waki’ar tabbas na ranakun 12-14/12/2015 yayi nasara akan mahukuntan Nijeriya, domin girman Saiyid Zakzaky ya kara baiyana cikin girmamawa. Sakon Sayyid Zakzaky Ya  isa inda ba ayi zato ba.
*14.Mutane da yawa suka gigice sa'ad da suka gan shi, Ya munana har ya fita kamannin mutum.*



Aranar 14/12/2017 da Sojoji da DSS suka fara yada hotunan ta’addanci da sukayi ga Saiyid Zakzaky hankalin kowanne daga mabiyansa ya tashi cikin gigicewa saboda yanda muka ga kamanninsa ya koma. Domin ba wanda ya zaci Saiyid Zakzaky zai rayu sai ‘yan kadan.


*15.Amma yanzu al'ummai da yawa za su yi mamaki a kansa, Sarakuna kuwa za su riƙe baki saboda mamaki. Za su gani su kuma fahimci abin da ba su taɓa sani ba.”
*

Amma kuma kowa ya sha mamakin ganin yanda al’amarin Saiyid Zakzaky ya kyautata. Alokacin mahukunta da Malaman da aka nuna masu Saiyid Zakzaky kwance a matsayin gawa sun rike baki dan mamakin ganin cigaba da rayuwarsa. Sun fahimci cewa tabbas shi na daban ne wanda basu san haka ba a baya ba,


*Ishaya 53:1.Wane ne zai gaskata abin da muka ji yanzu? Wane ne zai iya ganin ikon Ubangiji cikin wannan?*
Hakika mun gaskata wannan ikon na Ubangiji mai ban mamaki akan Siayid Zakzaky.


*2.Nufin Ubangiji ne bawansa ya yi girma Kamar dashe wanda yake kafa saiwarsa a ƙeƙasasshiyar ƙasa. Ba shi da wani maƙami ko kyan ganin Da zai sa mu kula da shi. Ba wani abin da zai sa mu so shi, Ba kuwa abin da zai ja mu zuwa gare shi.*


Da wannan waki’ar na 2015 Allah yayi nufin fadada da’awar Saiyid Zakzaky a fadin Nijeriya. Saiyid Zakzaky bai tara makami ba dan yakar kowa da zai sanya har mahukunta takalar sa domin jin tsoro:


*3.Muka raina shi, muka ƙi shi, Ya daure da wahala da raɗaɗi. Ba wanda ya ko dube shi. Muka yi banza da shi kamar shi ba kome ba ne.*


Mahukunta suna ganin sa a raine sai suka nuna ma Saiyid Zakzaky kiyayya. Ya daure ma duk cutarwarsu. Sunki duban halin da yake ciki, sukayi banza dashi duk da umarnin kotu akanshi na su sake shi, domin basu dauke shi a bakin komai ba sai suka ki bin umarnin kotu:


*4.Amma ya daure da wahala wadda a ainihi tamu ce, Raɗaɗin da ya kamata mu ne zamu Tasha shi. Mu kuwa muna tsammani wahalarsa Hukunci ne Allah yake yi masa.*


Duk da haka Saiyid Zakzaky ya daure ma wannan cutarwar, wacce mu magoya bayansa ne ya dace da ace mune muke shanta. A daidai lokacin da wahabiyawa suke tunanin duk wannan halin da Saiyid Zakzaky yake ciki Zunubin sa ne wai na zagin sahabbai da yin shi’anci:


*Ishaya 53:5.Amma aka yi masa rauni saboda zunubanmu, Aka daddoke shi saboda muguntar da muka aikata. Hukuncin da ya sha ya 'yantar da mu, Dukan da aka yi ta yi masa, ya sa muka warke.*


Duk wannan wahalar da Saiyid Zakzaky ya shiga fatan sa shine al’ummar wannan kasar su sami tsira, mu sami waraka daga halin kakanikayi da mahukunta suka jefa mu.


*6.Dukanmu muna kama da tumakin da suka ɓata, Ko wannenmu ya kama hanyarsa. Sai Ubangiji ya sa hukunci ya auko a kansa, Hukuncin da ya wajaba a kanmu.*


Jama’ar Nijeriya sun kasanc a cikin bata da baganniya, sai ga wannan waki’ar domin a fuskanto da jama’ar kasa zuwa ga wajibcin kalubalantar zaluncin azzaluman mahukunta, irin su Buhari:

*7.Aka ƙware shi ba tausayi, Amma ya karɓa da tawali'u, Bai ko ce uffan ba. Kamar ɗan rago wanda ake shirin yankawa, Kamar tunkiya wadda ake shirin yi wa sausaya, Bai ko ce uffan ba.
*


Mahukuntan Nijeriya sun nuna kuma suna ci gaba da nuna halin rashin tausayi akan Siayid Zakzaky, amma ya karbi hakan akan cewa daga Allah ne.


*8.Aka kama shi, aka yanke masa shari'a, Aka tafi da shi domin a kashe shi, Ba wanda ya kula da ƙaddararsa. Aka kashe shi saboda zunubin mutanenmu.*


Sun Kama Saiyid Zakzaky sun tafi dashi suka yanke masa hukuncin kisa akan makarkashiyar wasu cikin laifin da bai aikata ba:


*9.Aka yi jana'izarsa tare da maguye. Aka binne shi tare da masu arziki Ko da yake bai taɓa yin laifin kome, ko ƙarya ba.
*


Sun tsare Saiyid Zakzaky tare da tare da wadanda ake tuhunarsu da aikata laifin cin kudi da neman wargaza kasa, alhali shi Siayid Zakzaky bai aikata laifin komai ba. Kamar yanda mai shari’a Kolawale ya tabbatar da haka a ranar 2/12/16.


*10.Ubangiji ya ce, “Nufina ne ya sha wahala, Mutuwar kuwa hadaya ce domin ta kawo gafara, Saboda haka zai ga zuriyarsa, Zai yi tsawon rai, Ta wurinsa nufina zai cika.
*


Allah yayi nufin wannan wahalar da Saiyid Zakzaky ya sha, da kuma rasa yaransa da dimbin mabiaynsa sama da 1000 ya zama sanadin kawo sauki ga Najeriyawa. Zai ga zuriyarsa ta ragowar yaransa. Zaiyi tsawon rai domin ta hannunsa ne manufar Ubangiji na samun sauki ga mutanen Nijeriya zai tabata:


*11.Bayan shan wahalarsa, zai sāke yin murna, Zai fahimta wahalar da ya sha ba ta banza ba ce, Shi ne bawana, adali, Zai ɗauki hukuncin mutane masu yawa, Ya sa su zama mutanena amintattu.:


Takai ta kawo ran Saiyid Zakzaky zai faranta tare damu gaba daya, zamu gane wannan wahalar bata banza bace, domin da wannan waki’ar mun iya gane cewa Saiyid Zakzaky shine kadai adalin Bawa da zai iya kai Nijeriya zuwa ga tudun muntsira, domin samar da aminci ga ‘yan kasa. An kashe yaran sa 3 da mabiya sama da 1000:


Amma maganar shine akai hankali nesa ayi abind aya dace da hankali.
*12.Saboda haka zan ba shi matsayi mai girma, Matsayi a cikin manyan mutane masu iko. Da yardarsa ya ba da ransa Ya ɗauki rabon masu laifi. Ya maye gurbin masu zunubi da yawa, Ya kuwa sha hukuncin da ya cancanci masu zunubi. Ya yi roƙo dominsu.”*


Bamakawa Allah zai daukaka matsayin Saiyid Zakzaky ya sanya shi daga masu ikon zartarwa a Nijeriya. Domin da yardarsa ya yarda yasha wannan wahalar da take tamu ce. yana da damar barin gidansa tun a farkon faruwar waki’ar amma ya yarda ya zauna, cikin rokon Ubangijinsa cewa, Allah ya sanya jininsa ya zaman fansa ga wannan al’ummar ta Nijeriya.


Hakika bani da lafazi ko Kalmar dazan iya furtawa damin yin godiya ga Allah Ta’ala a bisa baiwarsa na hadani da wannan babban bawan nasa a matsayin jagorana. Fiye da in ce Alhamdulillah Rabil Alamin.
Ya Allah muna rokon ka  Kabarmu Da Saiyid Zakzaky a mafi dacewar lokaci daga gareka, albarkacin babban shugaban da muke sauraren baiyanarsa Imam Mahdi (A). Tare da dan’uwansa Annabi Isa (A)



Ya Allah ka kunyata masu fadin ko Sama da Kasa zasu bazasu saki Saiyid Zakzaky ba.
Dan’uwa a cikin addinin Kirista, na barka lafiya, sai mun hadu a cikin wani sakon kuma a cikin dai ita wannan Surar ta Ishaya dangane da mai ceto a karshen zamani, da Annabi Ishaya yace shine dan Yasse.


Muhammad Sani Ra’is, Funtua.
+2347034595991
31/5/2017

6/9/1438

2 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Hmmmm kunkur kunkus...., amma kunkai jahillan gaske, bara na tambayeka mana, shin littafin ishaya aka aikomuna ko alqur'ani? Ya akayi ishaya yasan sunan.Zakzaky kuma yasan garin da yake? Measa Annabi muhammad sallallahu alaihi wasallam bai bayarda labarin shi zakzakyba? Tambayar mamaki meyasa ishaya baibayarda labari haleepha na 4 ba syydna Aliyu kuma mupsan shima.Waki'ar ta abkamasa, shin kodai a mugunyar aqeedarku zakzaky yafi syydna Aliyune, tunda gashi har ishaya ya iya bayarda labarinsa amma baibayarda na syydna Aliyuba?,shin kur'ani da hadisi yakamata mukafa hujjah dashi ko wani littafi daban? Wace k'aruwa zakzaky yasamu bayan.Faruwar wannan suburbud'a da yasha shida magoya bayanshi bayan lalacewa da tambad'ewa?

    Daga karshe, amma gaskiya ka iya bayarda labari munajira wani episode

    ReplyDelete
  2. Hmmmm kunkur kunkus...., amma kunkai jahillan gaske, bara na tambayeka mana, shin littafin ishaya aka aikomuna ko alqur'ani? Ya akayi ishaya yasan sunan.Zakzaky kuma yasan garin da yake? Measa Annabi muhammad sallallahu alaihi wasallam bai bayarda labarin shi zakzakyba? Tambayar mamaki meyasa ishaya baibayarda labari haleepha na 4 ba syydna Aliyu kuma mupsan shima.Waki'ar ta abkamasa, shin kodai a mugunyar aqeedarku zakzaky yafi syydna Aliyune, tunda gashi har ishaya ya iya bayarda labarinsa amma baibayarda na syydna Aliyuba?,shin kur'ani da hadisi yakamata mukafa hujjah dashi ko wani littafi daban? Wace k'aruwa zakzaky yasamu bayan.Faruwar wannan suburbud'a da yasha shida magoya bayanshi bayan lalacewa da tambad'ewa?

    Daga karshe, amma gaskiya ka iya bayarda labari munajira wani episode

    ReplyDelete
Previous Post Next Post