-Sheikh Adamu Tsoho Jos
Shi ilimi ba karatu bane kawai ilimi haske ne, kada ilimin mai ilimi ko zakin bakin mai zaki ya rudeka, duk mutumin da ya zamo baya aiki da ilimin sa wannan fa yana da hadari kaje wajen sa ka dauki karatu shiyasa Allah yace "Babban abinci na hakika shine abinci ruhi", Wannan aya 'Falyanzurul insanu ala Da'ami' malaman tafsiri suka ce ba ana maganan abincin tuwo da miya bane ba shine kawai ba ana nufin abincin ruhi ne, kada ka bawa ruhinka gurbataccen abinci. To kuma daga cikin abinci ruhi shine ilimi, don haka kasan wajen wa zaka karbi ilimi. Shi ko ilimi ba'a samunsa sai ka gabatar damukaddima, menene mukaddiman Ilimi shine tsarkakan zuciya, ikilasi kyakkyawan manufa da hadafi.
Ba zaka nemi ilimi don kazo ka burge mutane ba, ba zaka nemi ilimi don kayi mukabala ayi jayayya kace ka kada wane ba, ba zaka nemi ilimi don kayi alfahari wa 'yan uwanka ba, kace wa ya kai ni kaza na haddace kaza nayi kaza-nayi-kaza. Zaka nemi ilimi ne domin shiriya, shi ilimi haske ne wanda Allah yake jefawa a zuciyar wanda yaso, kuma duk wanda Allah ya jefa mishi wannan hasken zaka ga da zarar ka nemi ilimi Allah yana karama Ilimin da kamala, in dai Malami na Allah ne zaka ganshi yana da tawadu'u tare da kankan da kai yana da kyawawan dabi'u da halaye.
Allah zai so shi, mutane zasu so shi hatta tsuntsu a sama ko kifi a cikin teku zai so shi, saboda zuciyar ta Tsarkaka. To kuma duk wanda yayi takawan nan Allah yace "Ittakullaha Wa Yu Allikumullah" to ba yadda za'ayi kayi takawannan Allah bai baka ilimi ba, in dai kayi takawan nan to lallai zaka samu ilimi. Shi Allah ba marauwaci bane kamar yadda yace in dai kayi takawan nan zaka samu ilimi kamar yadda take Allah (T) shine "Wajibul Wujud" a zatinsa kuma"Wajibul Wujud" shine ta dukkan jine babu rowa a tattare da Allah.
Don haka idan mutum ya zamo manufarsa shine ya raya kansa ya samu abinci da abin sha, ya ainihin girmama kansa shine manufar neman ilimi, to wannan fa ba zai zamo manufa na Allah ba. Kuma zai zamo tunda ba Allah aka nufa ba yadda za'ayi wannan hasken na Allah ya jefa a zuciya, sai a wayi gari maimakon haske ya shiga zuciyar mutum sai a wayi gari duhu ne daga shaidan sai ya shiga zuciya. Saboda haka idan kaje makaranta da sunan ilimi ba waccan mukaddima din duk abinda kake shaidan yana tare da kai. Koda cin abinci ne ko shan abin sha in bakayi bismillah ba zaka yi musharaka dashi.
Dole mutum ya kasance yana da tsarkakan zuciya, shi yasa wasun mu zasuyi Gwagwarmayan nan tun farko ba sun zo da tsarkakan zuciya bane, ba sun zo neman shiriya bane sai ya zamo suyi shekara da shekaru maimakon su bada gudumawa sai ya zamo suna zagon kasa ne ga addini suna fada da ma'abota addini. To insha Allah zamu tsaya a nan, wannan dai duk mukaddinma ne kafin Imam ya shiga mana ainahin babin ya zaka samu ilimi sahihi.
Daga Jawabin Sheikh Adamu Tsoho Jos wanda yayi ranar Lahadin da ta gabata a Hussainiyatu Zakzaky (H) Jos a lokacin Ta'alimin da ake gabatarwa duk sati a Unguwan Rogo dake Jos a cikin littafin ARBA'UNA HADITH na Imam Khomeini Hadisi na 23 wanda yake magana akan Ilimi.
--Idishia Jos.

Tags:
Taskar ilimi