ACADEMIC FORUM YANKIN KONTAGORA SUNKAI ZIYARAR BARKA DA SALLAH GA MANYAN MALAMAI TARE DA BASU KYAUTUTTUKA

ACADEMIC FORUM YANKIN KONTAGORA SUNKAI ZIYARAR BARKA DA SALLAH GA MANYAN MALAMAI TARE DA BASU KYAUTUTTUKA:

Daga Wakilanmu Na Yankin Kontagora
*(@Auwal M. Tukur)*
            &
*(@Shana Islam )*



Liman Malam Shehu Rimaye (Kontagora) yace "A kullum ina yiwa Malam Ibrahim Zakzaky Addu'a. Domin Manzon Allah yace bazaka taba cika mumini BA, har sai ka sowa dan uwa ka abinda kake sowa kanka.


Yan Academic Forum na yankin Kontagora sun kai ziyarar barka da Sallah. Ga wasu daga cikin manyan Malaman Darikar Tijjaniyya na garin Kontagora A Ranar Asabar 8/6/2019.

Ziyarar dai ta samu halartar yan uwa maza da mata . Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky na yankin na Kontagora. Abin burgewa a wannan ziyarar shine duk inda aka kai wannan ziyarar. Za ka ga suna nuna jin dadin su da wannan ziyarar. Tare da fatan alkhairi ga jagoran harkar Musulunci Sayyid Zakzaky (H).


Malaman da aka samu damar kawai ziyarar sune , Liman Malam Shehu Rimaye (limamin Masallacin Gidan Sarkin Kontagora),Malam Ibrahim Shehu,  Babbar Zawiyya Shehu Adamu Kontagora,Da kuma Khalifa Malam Sabi'u umar.Wanda duk cikar wadannan shehun nan, shehun nai ne na Darikar Tijjaniyya  da suke a cikin garin Kontagora. Kuma duk cikar su sunyi addu'a ta musamman ga Sayyid Zakzaky tare da fatan Allah ya fito da shi.


Daga karshe kuma ,Yan Academic Forum din sun karkare ziyarar tasu ne . A wurin wakilin Yan uwa almajiran Sayyid Zakzaky na garin Kontagora,wato Malam Ibrahim Imam. Inda ya ja hankalin yan uwan akan dagewa wurin neman ilimin Addini da kuma na Boko. Daga karshe ya rufe da Addu'a.


Daga Wakilanmu Na Yankin Kontagora
@Auwal M. Tukur
            &
@Shana Islam
8/6/2019
🌹🌹Happy Sallah🌹🌹
Zaidu Suleiman

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post