Danna domin karantawa kayi shere domin Wasu su amfana
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Anyi qoqarin boye gaskiya don canza haqiqanin addinin da Annabi (S) ya koyar kuma ya bar mana a bayansa.
Daga cikin hanyar da suka bi don aiwatar da wannan danyen aiki nasu shine suka ce wai an bar mana LITTAFIN ALLAH DA SUNNAH ne.
Duk da cewar Umar Bn Khaddab yayi watsi da wannan qaryar inda ya nuna cewa shi LITTAFIN ALLAH KADAI YA ISHE SU, wato Sunnar ma da suka iqirari ba sa buqata.
Abinda ya tabbata cikin littafan Sunnah shine LITTAFIN ALLAH DA IYALAN GIDAN ANNABI.
(1)- Ya zo cikin Sahihul-Muslim cewa, Manzon Allah (S.A W.W) ya fada cikin Khudbarsa a Ghadir Khum cewa;
" LALLE NI NA BAR MUKU NAUYAYAN ABUBUWA BIYU, LITTAFIN ALLAH DA TSATSONA. LALLE SU (biyun) VS ZA SU TABA RABUWA BA HAR SAI SUN RISKENI A TAFKINA."
-Muslim, J:7, Sh:122.
-Musnad Ahmad, J:3, Sh:14.
(2)- Baban Isah Al-Tirmudhi yace, Aliyu Bn Munziri Al-Kufiy ya bamu labari, Muhammad Bn Fudhai ya bamu labari, A'amashu ya bamu labari daga Adiyyata, daga baban Sa'id, da kuma A'amashu daga Hubaib Bn Abiy Thaabit, daga Zaid Bn Arqaam (R.A) yace, Manzon Allah (S.A.W.W) yace;
" LALLE NI NA BARI A CIKINKU ABINDA MATUQAR KUNYI RIQO DA SHI BA ZA KU BATA BA A BAYANA. 'DAYANSU YA FI GIRMA FIYE DA 'DAYAN; LITTAFIN ALLAH, MIQAQQIYAR IGIYA DAGA SAMA ZUWA QASA. 'DAYAN KUMA SHINE TSATSONA IYALAN GIDANA, BA ZA SU TABA RABUWA BA HAR SAI SUN RISKENI A TAFKINA, KUMA ZANYI DUBI NAGA WACCE IRIN MAYEWA KU KAYI MIN A CIKINSU."
-Tuhfatul-Ahwaz na Tirmidhi, J:10, Sh:289.
TAMBAYA
________
Dan Allah ku kuwa s ina ku ka samo KITABU WAS-SUNNAH?
Shin, ko maruwaita wannan hadisan, wato Muslim, Imam Ahmad da Tirmidhi maqaryata ne?
" HAATU BURHANAKUM IN KUNTUM SAADIQEEN!"
Tare da Ado Isah Guda
Tags:
Taskar ilimi