Sakataren OPEC, Janaral Mohammad Barkindo, ya bayyana cewa; abu ne mai wahala a iya hana yaduwar fetur din Iran a kasuwar duniya. Kamfanin dillancin labaran SHANA na Iran ne ya labarto wannan labarin a yau Alhamis.
Ya ce; “Babu bukatar na maimaita. Amma ba zai yiwu a iya dakatar da yaduwar fetur din Iran a kasuwar duniya ba.” Inji Barkindo a ziyarar da ya kai Tehran.
Rahotanni dai sun bayyana cewa; kasar Amurka ta gargadi kasashen duniya da su daina siyan fetur din Iran, ko kuma a kakaba musu takunkumi.
@Ishaq sagir magaji
1-5-209